Yadda Aka Saba Wasiyyar Ahmadu Bello Kan Birne Shi a Sokoto, an Gano Dalili
- Ana ci gaba da muhawara kan juyin mulkin 1966, musamman batun dalilin da ya sa aka birne Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto a Kaduna
- Masana tarihi sun bayyana dalilin birne Sardauna a Kaduna bayan kashe shi a juyin mulki wanda ya hana mayar da gawarsa Sokoto kamar yadda ya yi wasiyya
- Sheikh Abubakar Gumi ne ya jagoranci wankan gawar da sallar jana'izar Sardauna, inda aka birne shi a gidan Sarkin Musulmi da ke Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Yayin da ake tunawa da cikar shekaru 60 da juyin mulkin Janairun 1966, ana sake tattauna tasirin da lamarin ya haifar ga siyasar Najeriya da Arewa baki ɗaya.
Juyin mulkin ya yi sanadiyyar mutuwar shugabanni irinsu Firaminista Abubakar Tafawa Ɓalewa da Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da wasu fitattun ’yan siyasa.

Source: Getty Images
Dalilin birne Sardauna a Kaduna maimakon Sokoto
Masanin tarihi, Dr. Shuaibu Aliyu, a hirarsa da BBC Hausa ya yi tsokaci game da kisan Sardauna da kuma dalilin birne shi a Kaduna maimakon Sokoto.
Wani abu da ke jan hankali shi ne dalilin binne Sardauna a Kaduna, maimakon Sokoto, duk da cewa an mayar da sauran waɗanda aka kashe jiharsu.
Shuaibu ya ce tun Sardauna yana raye ya bayyana cewa yana so a birne shi kusa da kakanninsa a Sokoto, jihar da ita ce tushensa.
Dr. Shuaibu ya ce da kan shi marigayin ya je Sokoto, inda ya nuna wa makusantansa cewa yana so a birne shi a kusa da su kamar yadda aka saba yi a danginsu.
A game da yadda aka birne marigayin, Dr Shuaibu ya ce tun kafin rasuwarsa dama ya yi wasiyyar yadda yake so a birne shi.
Ya ce a daren da aka yikisan, Sarkin Musulmi ya so a mayar da gawar Sokoto, amma dokar ta-ɓaci ta hana shiga da fita daga Kaduna.
Ya ce:
"A daren ranar da aka kashe marigayin, washe gari, Sarkin Musulmi na wancan lokacin ya buƙaci a mayar da gawar Sardaunan zuwa Sokoto, amma sai ya kasance babu dama saboda an saka dokar ta-ɓaci."

Source: Original
A ina iyalan Ahmadu Bello suka rasu?
Saboda haka, aka ga babu wata dama face a birne marigayin a Kaduna, inda Sheikh Abubakar Gumi ya jagoranci yi masa wanka da sallar jana'iza.
Masanin tarihin ya kuma tabbatar da cewa daga baya an kwashe iyalan Sardauna zuwa Sokoto, inda suka ci gaba da rayuwa har suka rasu.
Ahmadu Bello Sardauna, haifaffen Sokoto, ya kasance Firimiyan Arewa daga 1954 zuwa 1966, kafin kashe shi a juyin mulkin Janairu 1966.
Kashe Sardauna ne tushen matsalar Najeriya
A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon Sanata Shehu Sani ya bayyana takaicinsa na kisan Sir Ahmadu Bello da sauran manyan 'yan siyasa a juyin mulkin 1966.

Kara karanta wannan
Duk da harin Amurka, 'yan Sokoto sun fadi yadda barazanar Bello Turji ke tarwatsa su
Sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya ya ce kisan ya zama tushen fitina da har yanzu ke addabar Najeriya.
'Dan siyasar ya ce Ahmadu Bello ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa jama’arsa da kasarsa ba tare da tara abin duniya ba.
Asali: Legit.ng

