Rashin Imani: An Watsa wa Dan Shekara 17 Acid a Hanyar zuwa Masallaci a Adamawa

Rashin Imani: An Watsa wa Dan Shekara 17 Acid a Hanyar zuwa Masallaci a Adamawa

  • Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta kama Idris Hamza bisa zargin watsa wa wani matashi dan shekara 17 ruwan acid a garin Yola
  • Matashin mai suna Walid Mohammed yana karbar magani a asibiti yayin da jami'an CID suke jan ragamar binciken domin tabbatar da adalci
  • Bincike ya nuna yadda hare-haren ruwan acid ke haifar da nakasa ta dindindin da matsananciyar damuwa ga wadanda abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Adamawa - Rundunar yan sandan Adamawa ta ƙaddamar da bincike kan yadda aka watsa wa wani matashi ɗan shekara 17, Walid Mohammed ruwan acid a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu.

Wannan ta'addanci ya jefa mazauna yankin cikin firgici, ganin yadda aka kai wa matashin harin sa'ilin da yake kan hanyarsa ta zuwa masallaci domin gudanar da ibada.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Wani dan Najeriya ya tada rigima a coci, ya fice daga addinin Kiristanci

'Yan sanda sun fara bincike kan watsa wa wani matashi acid a Adamawa
Taswirar jihar Adamawa, inda ake zargin an watsa wa dan shekara 17 acid. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An watsa wa matashi acid a Adamawa

Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 15 ga watan Janairu, 2026, in ji rahoton Punch.

A cewar Nguroje, lamarin ya faru ne a ranar 14 ga Janairu a unguwar Shagari Quarters, kuma matashin ne ya garzaya ofishin yan sanda na Shagari cikin matsanancin ciwo da firgici domin neman ɗauki.

Matashin ya bayyana wa jami'an tsaro cewa wani mutum mai suna Idris Hamza, wanda mazaunin unguwar Shagari ne, ya yi masa kwanton-ɓauna sannan ya watsa masa wani abu mai zafi da ake zargin ruwan acid ne.

'Yan sanda sun fara binciken watsa acid

A cikin sanarwar, SP Nguroje ya ce:

“Bayan samun rahoton, jami’anmu sun garzaya da matashin zuwa asibiti inda yanzu haka yake karɓar magani na musamman, sannan kuma tuni har an yi nasarar cafke wanda ake zargin.”

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Dankombo Morris, ya nuna bacin ransa kan wannan danyen aiki, inda ya ba da umarnin tura maganar zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jihar.

Wannan bincike zai karkata ne wajen gano asalin dalilin da ya sa Idris Hamza ya kai wa matashin wannan hari da kuma tabbatar da cewa doka ta yi aikinta yadda ya kamata.

Tasirin ruwan acid a jikin dan Adam

Legit Hausa ta fahimi cewa watsa ruwan acid a jikin mutum wani nau'i ne na ta'addanci wanda masu aikata shi ke yi da nufin yin lahani, gallazawa, ko ma kashe wanda suka farmaka.

Nazarin da masana kimiyya daga kwalejin NILEST da ke Zaria suka gudanar ya nuna cewa ruwan acid yana narkar da fatar ɗan adam ne cikin kankanin lokaci.

Rahoton nazarin da Legit Hausa ta karanta a shafin IJMRSTI ya nuna cewa idan har ba a yi gaggawar wanke acid da ruwa mai yawa ba, yana cinye fata ya ratsa har zuwa ƙasusuwa da sauran sassan jiki na ciki.

"Wannan hari ba kawai rauni na jiki yake haddasawa ba; yana barin waɗanda abin ya shafa da mummunan rauni na tunani, a cewar rahoton," cewar binciken.

Kara karanta wannan

Neman sulhu: Ƴan bindiga sun gindaya wa gwamnatin Katsina sharudda 8 masu tsauri

'Yan sanda sun ce za su gano bakin zaren watsa acid da aka yi wa wani matashi a Adamawa.
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Hare-haren acid a Adamawa da Edo

Yawancin waɗanda ake kai wa harin suna fuskantar kyama a cikin al'umma saboda yadda fuskarsu ke canzawa ko kuma rasa idanunsu baki ɗaya.

Rahotanni sun nuna cewa a watannin baya na shekarar 2025, an samu makamancin wannan hari a jihohin Edo da kuma Adamawa kanta, inda har yanzu wasu daga cikin waɗanda aka kai wa harin suke neman adalci.

A Edo, 'yan sanda suna farautar wani Timothy Gilbert, wanda ake zargin ya yi wa budurwarsa wanka da acid, yayin da a Adamawa aka sake bude binciken watsa wa wasu mata uku acid.

Hukuncin kotu kan laifin watsa acid

A wani labari, mun ruwaito cewa, an yankewa wani matashi hukuncin shekaru bakwai a gidan yari bisa zarginsa da aikata laifin cutar da budurwarsa da abokin nemansa.

An gano cewa, ya watsa musu ruwan ‘acid’ mai kone fata a lokacin da suke kwance a dakin otal, lamarin da ya jawo tashin hankali, har dai ta kai su gaban alkali.

Mai shari’a Oyindamola Ogala ta kama Agu da laifin cutar da mutum biyu, inda da kansa ya amsa cewa ya aikata laifin, wannan ya sa ta yanke masa hukuncin da ya dace da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com