Daga Urumba zuwa Uromi: Lokutan da Aka Tare Hausawa a Kudu, Aka Kashe Su Haka Siddan

Daga Urumba zuwa Uromi: Lokutan da Aka Tare Hausawa a Kudu, Aka Kashe Su Haka Siddan

Al’ummar Hausawa daga Arewa da ke zaune a Kudancin Najeriya na fuskantar hare-hare da kisan gilla, hakan na haddasa asarar rayuka da dukiyoyi ba tare da laifi ba.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin-City, Edo - Al'ummar Hausawa ko yan Arewa da ke zama a Kudancin Najeriya na ci gaba da fuskantar barazana.

Mafi yawansu na fuskantar hare-hare da ke jawo musu asarar rayuka da dukiyoyi duk lokacin da wani karamin abu ya faru a yankin da suke zama ko kasuwanci.

Yadda aka kashe Hausaw a Edo da Anambra
Gwamna Charles Soludo na Anambra da takwaransa na Edo, Monday Okpebholo. Hoto: Charles Chukwuma Soludo, HE Sen. Monday Okpebholo.
Source: Facebook

Yadda ake kai wa Hausawa hari a Kudu

Rahoton Punch ya bayyana cewa mafi yawanci ana kashe 'yan Arewa da ke zama ko kasuwanci a Kudu ba tare da sun aikata laifin komai ba.

Lamarin na ci gaba da ta da jijiyoyin wuya a tsakanin al'ummar Arewa da suke ganin ana cin zarafinsu ba tare da kariya ba.

Kara karanta wannan

Daga barin kurkuku, AbdulRasheed Maina ya fara tone tone kan Abubakar Malami

Kungiyar dattawan Arewa na daga cikin masu sukar hukumomi kan hare-haren da ake kai wa Hausawa a Kudu da ta kira da rashin adalci.

Mai magana da yawun kungiyar ACF, Muhammad Baba, ya fitar da wata sanarwa kan lamarin wanda Premium Times ta samu inda yake sukar cewa ana sakaci kan lamarin.

Ya ce ana kai wa direbobi mummunan hari ba tare da wani dalili ba, lamarin da ke haddasa kisan gilla, ƙone motoci da kuma wawashe kayan da ake safararsu, kamar abinci da shanu.

Legit Hausa ta duba wasu daga cikin kisa hare-haren da aka kai wa yan Arewa a yankin Kudu.

1. Kisan Harira da 'ya'yanta a Anambra

A ranar 25 ga watan Mayu, 2022 wasu miyagu da ake zargin yan kungiyar IPOB ne suka hallaka wata mata da 'ya'yanta hudu daga Arewacin Najeriya.

Mijinta wanda ya rasa matarsa mai tsohon ciki da 'ya’ya hudu a jihar ya bayyana cewa ya ji kamar ya yi hauka sakamakon tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki.

Tsagerun yan bindiga da ake zaton yan kungiyar awaren IPOB ne suka kai farmakin inda suka hallaka mutane 12 ciki harda matar mai tsohon ciki, Harira Jibril da yaranta.

Kara karanta wannan

Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame

Mijin matar da aka kashe a harin ya ce an kashe iyalin nasa ne a lokacin da suke kan hanyar su ta dawowa daga ziyarar da suka kai a yankin Orumba ta Arewa a jihar Anambra.

Gwamna ya ji haushin kashe Harira da 'ya'yanta a Anambra
Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo. Hoto: Charles Chukwuma Soludo.
Source: Facebook

2. An hallaka 'yan Arewa a Uromi

An kashe wasu matafiya 16 daga Arewacin Najeriya sakamakon zargi maras tushe da aka yi musu yankin Uromi da ke jihar Edo.

‘Yan sa-kai sun zarge su da laifin garkuwa da mutane, lamarin da ya haddasa kashe su ba tare da bincike ba ranar Asabar 28 ga watan Maris, 2025.

Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta kama mutane da dama da ake zargi da hannu a lamarin.

Mummunan harin ya jawo suka daga sassan kasar baki daya har ma daga cikin 'yan Kudancin Najeriya da suke ganin harin a matsayin karshen rashin imani kenan.

Gwamna ya gana da Abba kan kisan Hausawa a Edo
Gwamna Monday Okpebholo yayin ziyara ga Abba Kabir bayan kisan Hausawa a Edo Hoto: Sanusi Bature D-Tofa.
Source: Twitter

3. Kashe direbobin Arewa a Imo

Wasu ƴan bindiga sun kashe direbobi biyu tare da kona tirela a jihar Imo, kamar yadda hukumar NURTW ta tabbatar da lamarin.

NURTW ta zargi ƴan IPOB da kai harin, inda aka ce sun tare hanya tare da buɗe wuta kan direbobin, sannan suka kone gawarsu da motar.

Kara karanta wannan

Kano: Yadda ake kyamatar yan uwan Fatima da aka yi wa kisan gilla a zaman makoki

Manya daga Arewa na kira ga kungiyar gwamnonin yankin da ta dauki mataki kan irin asarar rayukan 'yan Arewa da ake yi a Kudu.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar 10 ga watan Yunin 2025 da misalin karfe 10:30 na safe a karamar hukumar Okigwe da ke jihar.

An kona direbobi daga Arewa a Imo
Babbar tirelar da ake zargin 'yan IPOB sun kona tare da direbobin da ke ciki a Imo. Hoto: UGC.
Source: UGC

4. An kai hari kan Hausawa a Ekpoma

Wasu fusatattun matasa sun fatattaki Hausawa a kasuwar dabbobi ta Ekpoma, inda suka yanka awaki sakamakon zanga-zanga.

Lamarin ya jawo asarar dukiyoyi daga bangaren yan kasuwar wadanda suka fito daga yankin Arewacin kasar a ranar Asabar ga watan Janairun 2026.

Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai kira da a kwantar da hankali domin kauce wa ramuwar gayya.

’Yan sanda sun ce an ceto mutane tara da aka sace bayan amfani da na’ura inda aka tilasta wa masu garkuwa tserewa.

Gwamna ya yi Allah-wadai da hari kan Hausawa a Edo
Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo yana jawabi ga al'umma. Hoto: HE Sen Monday Okpebholo.
Source: Twitter

IPOB ta musanta kisan Harira a Anambra

A wancan lokaci, kun ji cewa Kungiyar IPOB ta nesanta kanta daga kisar Harira Jubril da yaranta hudu da wasu Hausawa a Anambra.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna ya sha alwashi, zai ceto mutum sama da 170 da 'yan ta'adda suka sace

Haramtaciyyar kungiyar na masu neman kafa Biafra, ta bakin kakakinta, Emma Powerful, ta ce babban laifi ne kisar mace mai juna biyu a kasar Igbo.

Powerful ya yi ikirarin an dauko hayan makasan Fulani an turo su yankin domin su rika kisa a kuma danganta kisar da IPOB don bata mata suna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.