Wata Sabuwa: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Wasu Sauye Sauye da Sababbin Dokokin Haraji
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kananun sauye-sauyen da aka samu ba za su rage komai a sababbin dokokin haraji ba
- Shugaban kwamitin gyara fasalin haraji na shugaban kasa, Taiwo Oyedele ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Legas
- Wannan na zuwa ne bayan ce-ce-ku-cen da aka yi kan banbancin dokokin haraji da Majalisa ta amince da su da wadanda ke hannun gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa an sami wasu kananan sauye-sauye a sababbin dokokin haraji hudu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu.
Shugaban kwamitin sake fasalin haraji na shugaban kasa, Taiwo Oyedele, ya ce kananan sauye-sauye da aka samu ba za su yi wani tasiri mai girma ga manufar dokokin haraji ba.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kura na ci gaba da tashi kan dokoki hudu na gyara tsarin haraji da suka fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026.

Kara karanta wannan
Shugaban kwamitin harajin Tinubu na tsaka mai wuya, an fara barazanar tura shi lahira
Dokokin sun hada da Dokar kafa Hukumar Karbar Haraji ta Kasa (NRS), Dokar Hukumar Hadin Gwiwa ta Harajin Najeriya, Dokar Gudanar da Haraji, da kuma Dokar Harajin Najeriya kanta.
Ina aka samu matsala a dokar haraji?
Rigimar ta samo asali ne biyo bayan zargin cewa akwai bambanci tsakanin dokokin da aka wallafa a kundin gwamnati da kuma takardun da Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da su.
A zaman majalisa na watan Disamba, dan majalisa, Hon Abdussamad Dasuki (PDP, Sokoto) ya tayar da maganar, inda ya ce an keta alfarma da hakkinsu na 'yan majalisa.
Ya bayyana cewa bayan ya kwashe kwanaki uku yana nazarin kundin da gwamnati ta fitar, ya gano cewa abin da ke ciki ba shi ne abin da suka tattauna, suka kada kuri’a, kuma suka amince da shi ba.
Kiraye-kirayen dakatar da dokar haraji
Wannan takaddama ta sa 'yan adawa kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da dokokin har sai an tantance gaskiyar lamarin, kamar yadda Punch ta kawo.
To sai dai, gwamnatin tarayya ta dage cewa lallai dokokin dole su fara aiki daga ranar 1 ga Janairu kamar yadda aka tsara.

Kara karanta wannan
Shirin tsige Gwamna Fubara a Majalisa ya gamu da tangarda, 'yan Majalisa 2 sun canza tunani
Don fayyace gaskiya, Majalisar Wakilai ta fitar da sahihan kwafi (CTC) na dokokin guda hudu a ranar 3 ga watan Janairu, 2026

Source: Twitter
Wadanne sauye-sauye aka samu?
Da yake karin haske a birnin Legas a ranar Laraba, Taiwo Oyedele ya bayyana cewa sauye-sauyen da ake magana a kai ba su shafi ainihin kashin bayan dokokin ba.
Ya bayyana cewa duk da hayaniyar da ake yi na cewa an sauya wasu abubuwa, wadancan sassa ba su da yawa kuma ba su taba muhimman batutuwan da suka shafi al'umma ba.
Oyedele ya ce:
"Abin da zan iya fada muku shi ne, matsalar da aka samu ba mai yawa ba ce, domin duk wannan maganar ta cewa an sauya ko ba a sauya ba, ba abin damuwa ba ne
"Akwai wasu 'yan abubuwa kadan wadanda ba za su shafi manyan batutuwan da mutane ya kamata su sani ba. Babu abin da aka sauya game da adadin haraji."
An fara yi wa Taiwo Oyedele barazana
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban kwamitin gyara haraji na shugaban kasa, Taiwo Oyedele ya ce rayuwarsa na fuskantar barazana saboda kokarin da yake yi.
Mista Taiwo Oyedele ya ce wasu mutane sun fara bazanar raba shi da duniya saboda rawar da ya taka wajen sauya dokokin haraji a Najeriya.
Oyedele ya bayyana cewa aiwatar da sauye-sauye, musamman na haraji, abu ne mai matuƙar wahala domin yana shafar manyan masu ruwa da tsaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
