Akwai Tagomashi: Najeriya Ta Kulla Sabuwar Yarjejeniya da Daular Larabawa
- Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun rattaba hannu kan yarjejeniyar CEPA don bunƙasa kasuwanci da zuba jari
- A sanadiyyar haka, kasar UAE za ta cire haraji kan sama da kayayyaki 7,000 daga Najeriya, musamman na noma da masana’antu
- Haka kuma an jero bangarorin da Daular Larabawan za ta kwashi riba a yarjejeniyar da ake sa ran za ta amfani kasashen biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun kulla yarjejeniyar haɗin gwiwar tattalin arziki ta 'kasa da ƙasa (CEPA).
Ana sa ran yarjejeniyar za ta sauya fasalin alaƙar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu tare da samar da fa’ida kai tsaye ga ‘yan kasuwa, kwararru da ma’aikata a Najeriya.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa an cimma wannan yarjejeniya ne bayan dogon tattaunawa da jajircewa, ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari ta Tarayya (FMITI).
Najeriya ta shiga yarjejeniya da UAE
Thisday ta wallafa cewa Najeriya ta kulla wannan yarjejeniya a ƙarƙashin Minista, Jumoke Oduwole. Yarjejeniyar ta bai wa kayayyaki da ayyukan Najeriya damar shiga kasuwannin UAE cikin sauƙi.
Haka kuma a cikin yarjejeniya za ta jawo jarin kasashen waje da kuma tallafa wa manufofin bunƙasa tattalin arzikin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kayayyakin noma da na masana’antu irin su kifi, hatsi, auduga, magunguna da sinadarai za su shiga kasuwar UAE ba tare da biyan haraji ba.
A cikin shekaru uku zuwa biyar masu zuwa, UAE za ta cire haraji kan injina, motoci, na’urorin lantarki, tufafi da kayan daki daga Najeriya.
Haka kuma, ‘yan kasuwar Najeriya za su iya kafa kamfanoni, rassan kamfani da a UAE. Masu ziyartar kasuwanci daga Najeriya za su iya zama a UAE har zuwa kwanaki 90 cikin watanni 12.
Bayan haka, shugabanni da kwararru na kamfanoni za su iya komawa tare da kamfanoninsu na tsawon shekaru uku masu sabuntawa.
Najeriya ta samu fahimtar juna da Daular Larabawa
Yarjejeniyar ta kuma magance tsofaffin ƙalubale da ke hana zuba jari kai tsaye daga waje (FDI), tare da ba wa masu zuba jari na UAE kwarin gwiwa su saka jari a muhimman sassan tattalin arzikin Najeriya.
Rahoton ya bayyana cewa wannan zai taimaka wajen ƙarfafa masana’antu, inganta sufuri da dabarun jigilar kaya, da samar da ayyukan yi ga matasa.

Source: Facebook
A ƙarƙashin yarjejeniyar, Najeriya za ta cire haraji kan kusan kayayyaki 6,000, inda za a cire 60% nan take, sauran kuma a hankali cikin shekaru biyar.
Wadannan kayayyaki sun fi shafar kayan masana’antu kamar su injina yayin da jerin kayayyakin da aka haramta shigo na nan daram.
A bangaren ayyuka, Najeriya ta yi alkawari kan ayyuka 99 a fannoni 10 da suka hada da kasuwanci, sadarwa, sufuri, harkokin kudi, gine-gine, lafiya, muhalli, wasanni da yawon bude ido.
UAE ta tsaurara matakan shiga kasarta
A baya, kun ji cewa hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun ƙara tsaurara sharuddan ba da biza ga ‘yan Najeriya, lamarin da ya fi shafar masu shirin tafiya Dubai yawon buɗe ido.
Rahotanni sun nuna cewa sababbin matakan sun haɗa da dakatar da ba da sabbin bizar yawon buɗe ido ga wasu rukunin ‘yan Najeriya, musamman matasa kuma har an sanar da wakilan kamfanonin tafiye-tafiye.
An tabbatar da cewa sababbin ka’idojin sun fi shafar ‘yan Najeriya masu shekaru tsakanin 18 zuwa 45, inda aka ce ba za a ba su bizar yawon buɗe ido ba sai dai idan suna tare da abokin tafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


