Saudiyya Ta Hango Matsala, Ta Bayyana Abin da ke Kara Rura Wutar Matsalar Tsaro a Najeriya

Saudiyya Ta Hango Matsala, Ta Bayyana Abin da ke Kara Rura Wutar Matsalar Tsaro a Najeriya

  • Kasar Saudiyya ta bayyana cewa watsi da marayu da yara marasa galihu na daga cikin abubuwan da ke rura wutar matsalar tsaro a Najeriya
  • Ta gargadi gwamnatin Najeriya kan illar barin yara suna gararamba a gari, tana mai cewa hakan barazana ce ga tsaron kasar Afrikar
  • Saudiyya ta zakulo marayu sama da 1,000 daga addinin Musulunci da Kiristanci, ta ba su horo da jarin kama sana'a domin dogaro da kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumomin kasar Saudiyya sun gargadi gwamnatin Najeriya cewa, yin watsi da marayu da yara marasa galihu na iya zama babban barazana ga tsaron kasar.

Saudiyya ta bayyana cewa duba da yadda miyagu za su iya amfani da su cikin sauki saboda rashin abin yi, barin marayu da yara marasa galihu na gararamba a gari hatsari ne ga Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kashe Naira biliyan 40 a zamanantar da gadar Legas da CCTV

Sarki Salman.
Sarkin kasar Saudiyya, Salman Bin Abdul'Aziz Hoto: Inside The Haramain
Source: Facebook

Kasar Saudiyya ta tallafa wa marayu a Najeriya

AIT News ta ruwaito cewa wannan gargadi ya fito ne daga wakilan kasar ta Saudiyya yayin wani shirin tallafawa marayu sama da 1,000 a jihar Kwara.

Wannan tallafi na zuwa ne a matsayin goyon baya ga kokarin gwamnatin tarayya na rage radadin talauci da inganta rayuwar marayu a fadin Najeriya.

Yayin da yake jawabi a wurin raba kayan abinci da na dogaro da kai a Ilorin, babban birnin Kwara, shugaban shirin tallafawa marayu na Saudiyya, Farid Salman, ya fadi wasu manufofin shirin.

Ya bayyana cewa an tsara wannan shiri ne don biyan bukatun yau da kullum na yara da matasa marasa galihu, tare da koya musu hanyoyin dogaro da kansu.

Abin da Saudiyya ke ganin yana lalata tsaro

Ya jaddada cewa yin watsi da yara masu rauni babban hadari ne ga al'umma baki daya, domin za su iya karar rura wutar rashin tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan

A karon farko, Fubara ya yi magana ga al'ummar Rivers game da shirin tsige shi

Salman ya bayyana cewa an horar da wadanda suka amfana da tallafin a fannoni daban-daban da suka hada da dinki, girke-girken abinci da fasahar zamani.

Bayan horarwar, an raba musu kayan aiki da jarin fara sana'a domin ba su damar fara sana'o'insu na dogaro da kai, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Shugaba Bola Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja Hoto: @ananuga1956
Source: Twitter

An tattaro cewa marayu fiye da 1,000 ne suka ci moriyar wannan shiri, wadanda aka zakulo daga gidajen marayu na Musulmi da na Kirista, da nufin raba su da yawo a kan tituna don nisantar da su daga gurbatacciyar tarbiya.

Masu kula da gidajen marayun da suka amfana sun bayyana wannan tallafi a matsayin wanda ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa, inda suka ce hakan zai rage nauyin da ke kansu kwarai da gaske.

Gidauniyar Saudiyya ta bude gidan marayu

A wani labarin, kun ji cewa gidauniyar Albidairi daga kasar Saudiyya ta gina gidan marayu da babban masallaci a jihar Kano domin taimaka wa Musulmai.

Gidauniyar Albidairi ta yi wannan aikin alheri na gina masallaci da gidan marayu ne ne a yankin Langel da ke Karamar Hukumar Tofa, a Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabwa gidauniyar bisa wannan aikin alheri, wanda ya bayyana a matsayin aikin da ake bukatar karin iriinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262