'Harin Sojojin Amurka a Najeriya Ya Kashe Lakurawa 155,' Rahoto
- Rahoto ya bayyana cewa hare-haren soji da Amurka ta kai a Sokoto a watan Disamba, 2025 sun yi sanadin mutuwar Lakurawa sama da 150
- An ce hare-haren sun shafi yankuna uku ne, inda aka yi ikirarin cewa an yi amfani da makamai masu linzami daga teku tare da haɗin gwiwar Najeriya
- Sai dai wani rahoton tsaro na daban ya musanta wannan ikirari, yana cewa babu shaidar cewa an kashe ‘yan ta’addan Lakurawa a wurin harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Wani rahoto da wata kafar yada labarai ta ƙasashen waje ta wallafa ya yi ikirarin cewa hare-haren soji da Amurka ta kai a jihar Sokoto sun kashe ‘yan ta’addan Lakurawa 155 a watan Disamba, 2025.
Rahoton ya ce hare-haren sun gudana ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaron Najeriya, a wani mataki na ƙara matsin lamba kan ƙungiyoyin ta’adda da ke addabar wasu sassan Arewa maso Yamma.

Source: Getty Images
Rahoton da kafar New Humanitarian ta fitar ne ya yi ikirarin cewa harin Amurka a Najeriya ya yi nasara tare da fadin adadin Lakurawa da aka kashe.
Sai dai ikirarin ya janyo muhawara bayan wata kafar bincike ta daban ta fitar da rahoto mai karo da wannan bayani, inda ta ce babu hujja da ke nuna cewa an kashe Lakurawa a harin.
Yadda Amurka ta kai hari Najeriya
A cewar rahoton, hare-haren sun shafi ƙananan hukumomin Isa, Tangaza da Tambuwal a jihar Sokoto, duk da cewa Tangaza ce aka fi sani da kasancewa cibiyar Lakurawa.
Rahoton ya bayyana cewa an yi amfani da makamai masu linzami na Tomahawk, waɗanda aka harba daga wani jirgin ruwan yaƙi na Amurka da ke Tekun Guinea.
An ce harin ya auku ne sau biyu a wuri guda, inda harin farko ya kashe kimanin ‘yan ta’adda 30, sannan bayan sauran suka taru domin taimaka wa waɗanda suka jikkata, aka sake kai hari na biyu wanda ya hallaka yawancinsu.
Adadin Lakurawa da Amurka ta kashe
Rahoton ya yi ikirarin cewa jimillar Lakurawa 155 ne suka mutu sakamakon hare-haren, ciki har da wasu 19 da suka jikkata a farko amma daga bisani suka rasu.
Jaridar The Sun ta wallafa cewa an ce fiye da Lakurawa 200 sun ɓace mako guda bayan harin, lamarin da ya ƙara jefa tsoro a yankin.
Bugu da kari, rahoton ya ce wani babban kwamandan Lakurawa mai suna Dando Sibu ya tsira daga harin, saboda ya bar wurin mintuna kaɗan kafin harin na biyu.
An musa nasarar harin Amurka a Najeriya
Sai dai wani rahoto da kafar bincike mai yada labarai kan tsaro, HumAngle ta fitar ya ce ikirarin kashe Lakurawa ba gaskiya ba ne.
Rahoton da ta fitar ya bayyana cewa ta tattara bayanai daga shaidun gani da ido da mazauna yankin Bauni, inda aka ce harin ya auku.
A cewar mazauna yankin, Lakurawa sun bar wurin tun kafin a kai harin, kuma babu wata alama da ke nuna cewa an kashe ko an jikkata su.

Source: Original
Har yanzu ana jiran Najeriya da Amurka su fadi adadin 'yan ta'addan da aka kashe ko nuna hotunan barnar da aka yi a wajen.
Amurka ta kai hari kasar Venezuela
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta kai hari kasar Venezuela tare da kama shugaban kasa Nicolas Maduro.
Shugaba Donald Trump ne ya sanar da kai harin tare bayyana cewa sojojin Amurka sun samu nasara ba tare da tangarda ba.
Amurka ta kai harin ne bisa zargin kasar Venezuela da safarar kwaya, abin da shugaba Nicolas Maduro ya sha karyatawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


