Ana Shirin Sakin Ƴan Ta'adda 70, Sun Laftawa Manoma a Kano da Katsina Haraji

Ana Shirin Sakin Ƴan Ta'adda 70, Sun Laftawa Manoma a Kano da Katsina Haraji

  • Yan bindiga sun ƙara sako manoma a gaba inda suka yanka masu na harajin girbin N50,000 kan kowace eka a Kano da Katsina
  • Manoma na fuskantar barazana idan suka ki bin kuɗin da ya haɗa da lalata masu amfanin gona da kai masu munanan hare-hare
  • Wannan na zuwa a yayin da gwamnatin jihar Katsina ta kammala shirin sakin mutane 70 da ake zargi da alaƙa da ’yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyoyin ’yan bindiga da ke aiki a wasu sassan jihohin Kano da Katsina na tilasta wa manoma biyan harajin noma kafin girbi amfanin gonakinsu.

A yanzu haka, ƴan ta'addan na karɓar N50,000 kan kowace eka daga manoman rake, lamarin ya shafi har manoman masara.

Kara karanta wannan

Fubara: Majalisar dokokin Ribas ta ja kunnen masu yunkurin hana ta tsige Gwamna

Yan ta'adda sun sako manoman Katsina da Kano a gaba
Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf a yayin wani taro a Kano Hoto: Dr. Umaru Dikko Radda
Source: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa ana zargin cewa waɗannan ƙungiyoyi sun kafa wata hanya ta mulki mai zaman kanta a muhimman dazuzzuka na yankin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a waɗannan wurare ne ƴan ta'addan ke karɓar kuɗin haraji tare da tsoratar da al’umma.

Yan ta'adda na karban haraji wajen manoma

Aminiya ta ruwaito cewa bincike ya nuna cewa ’yan bindigan sun kafa sansani a dajin Rugu da ke ƙaramar hukumar Faskari a Katsina, da kuma dajin Falgore a ƙaramar hukumar Doguwa ta Kano.

A waɗannan wurare, suna karɓar abin da suka kira “harajin gona” daga manoma, tare da yin barazana ga duk wanda ya ƙi bin umarninsu na biyan kuɗin

Rahoton ya nuna cewa manoman da suka ƙi biyan harajin na fuskantar tsoratarwa, ana lalata amfanin gonarsu, har ma da yi musu barazanar kai hari.

Wannan lamari ya tilasta wa manoma da dama barin gonakinsu gaba ɗaya, lamarin da ke barazana ga samar da abinci a yankin da Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Shugaban ƙaramar hukuma a Binuwai ya nemi ɗauki kan karuwar ƴan ta'adda

Yan ta'adda na cin karensu ba babbaka

Manoman rake su ne suka fi shan wahala a halin yanzu, sai dai noman masara ma na cikin wadanda ke fuskantar muzgunar mutanen.

Rahotanni sun ce waɗannan dazuzzuka na cikin muhimman yankin samar da abinci tsakanin jihohin Kano da Katsina.

Wannan yankin na samar da rake da masara zuwa manyan kasuwanni irin su Kasuwar Dawanau a Kano da ake fitar wa ɓangarori da dama na duniya.

Ana zargin yan ta'addan na aikinsu a kusa da shingen tsaro
Dakarun sojojin Najeriya (H), jiragen yaki na shawagi (D) Hoto: Nigerian Airforce HQ
Source: Facebook

Duk da kasancewar wuraren bincike da shingayen sojoji da ’yan sanda a titin Falgore, rahoton ya nuna cewa ’yan bindigan na aiki a kilomita biyar kacal daga wuraren shingen tsaro. Wasu mazauna yankunan da manoma sun bayyana halin da ake ciki a matsayin karɓe iko a hankali, inda ’yan bindiga ke kafa dokoki, tare da mallakar harkokin tattalin arzikin yau da kullum ba tare da wata turjiya ba.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatocin jihohin da abin ya shafa ko kuma hukumomin tsaro ba.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Matakai 8 da majalisar Rivers za ta bi domin tsige Gwamna Fubara

Za a saki yan ta'adda a Katsina

A baya kun ji cewa, Gwamnatin Dikko Radda a jihar Katsina ta kare matakin sakin mutane 70 da ake zargi da alaƙa da ayyukan ’yan bindiga.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dakta Nasir Mu’azu, ya ce an ɗauki matakin sakin ne bisa yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ’yan bindigar da suka tuba da al’ummomin da rikicin tsaro ya shafa.

Nasir Mu’azu ya bayyana cewa yarjejeniyar zaman lafiyar da ta shafi aƙalla ƙananan hukumomi 15, ta haifar da sakin kusan mutane 1,000 da aka yi garkuwa da su daga hannun ’yan bindiga da suka ce sun tuba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng