'Yan Bindiga na Shirin Kai Hari Ranar Talata, Ƴan Sanda Sun Gaggauta Ɗaukar Mataki
- Rundunar yan sandan jihar Oyo ta tsaurara tsaro a garin Ikoyi-Ile bayan 'yan bindiga sun aiko da takardar barazanar kai hari ranar 20 ga Janairu
- A cikin wasikar, 'yan bindigar sun yi barazanar saukar da bala'i a kan al'ummar Ikoyi-Ile, tare da jaddada cewa mutanen garin su zama cikin shiri
- Kwamishinan 'yan sanda Femi Haruna ya ba da umarnin gudanar da sintiri na sa'o'i 24 domin kare rayukan mazauna yankin Oriire baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Rundunar 'yan sandan Jihar Oyo ta tsaurara matakan tsaro sosai a garin Ikoyi-Ile da ke ƙaramar hukumar Oriire, biyo bayan wata wasiƙar barazana da aka tsinta.
Wasiƙar, wadda aka bari a gaban wani gida a cikin garin, ta gargaɗi mazauna yankin da su shirya wa gagarumin hari da aka tsara kai masu ranar 20 ga Janairu, 2026.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun rubuta wasikar kai hari
Sakon da ke cikin wasiƙar, wanda ke cike da tsoratarwa, da aka rubuta da harsunan Yarbanci da Turanci, ya nuna cewa:
“Daga 'yan bindiga:
"Za mu farmake ku a ranar 20 ga Janairu, 2026, lallai ku shirya wannan farmakin. Za mu saukar da bala'i da masifa a kanku, kuma zuwan mu zai sanya hawayenku ya kwarara, rayuwarku ta shiga radadi marar misaltu, ya ku mutanen garin Ikopyi-lle, jihar Oyo.
"Ku shirya zuwanmu."
Wannan barazana ta tayar da hankulan mazauna yankin, musamman duba da cewa a farkon wannan mako, wasu mahara mutum 12 sun kai hari a yankin Oloka, inda suka kashe jami’an kula da gandun daji guda biyar a ofishinsu kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.
Matakan ko-ta-kwana daga rundunar 'yan sanda
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Oyo, Olayinka Ayanlade, ya bayyana cewa kwamishinan 'yan sanda, Femi Haruna, ya ba da umarnin tattara dukkan jami’an leken asiri da na runduna ta musamman domin fuskantar wannan barazana.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, rundunar 'yan sandan ta ce ta riga ta fara gudanar da bincike na tsanaki don gano asali da kuma sahihancin wasiƙar.
Sanarwar ta kuma ce an baza jami’an tsaro don yin binciken ababen hawa da sintiri na sa'o'i 24 a Ikoyi-Ile da daukacin kauyukan cikinta.
Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa an riga an tsara yadda jami’ai za su mamaye yankin domin toshe duk wata hanya da maharan za su iya bi wajen kai farmaki.

Source: Original
'Yan sanda sun nemi hadin kan jama'a
Rundunar tana bincikar dukkan mutanen da ke da alaƙa da gano wasiƙar don samun ƙarin bayanan da za su taimaka wajen dakile harin, in ji rahoton The Nation.
Ayanlade ya bukaci mazauna jihar da kada su firgita, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali, domin 'yan sanda na nan daram a kasa.
Haka zalika, an yi kira ga jama'a da su kasance masu sanya idanu sosai a unguwanninsu. Rundunar ta jaddada cewa samar da sahihan bayanai akan lokaci shi ne mabuɗin nasara ga jami'an tsaro.
Don haka, an bukaci mazauna yankin su garzaya ofishin 'yan sanda mafi kusa idan suka ga wani mutum ko motsi da ba su yarda da shi ba.
'Yan ta'adda 11 sun mika wuya
A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai dake yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta samu gagarumar nasara a Borno.
Rundunar ta ce dakarunta sun kashe ’yan ta’adda takwas, sun kama masu kai musu kayan abinci da man fetur guda biyu, yayin da wasu miyagun 11 suka miƙa wuya.
Kakakin rundunar, Sani Uba ya ce waɗannan nasarori sun biyo bayan matsin lamba da dakarun soji suka yi wa ’yan ta’addan a sassanoninsu daban daban da ke a Jihar Borno.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


