Akwai Matsala: Masana Sun Hango Babban Kalubale da Tinubu Zai Iya Fuskanta a 2026

Akwai Matsala: Masana Sun Hango Babban Kalubale da Tinubu Zai Iya Fuskanta a 2026

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta gabatar da daftarin kasafin kudin 2026 na Naira tiriliyan 58.18 ga majalisa, wanda ya dogara ga danyen mai
  • Tarihi ya nuna cewa a duk lokacin da gwamnati ba ta samu kuɗin shigar da take fata ba, ayyukan more rayuwa ne ke fara shan wahala
  • Masana dai sun ankarar da Tinubu game da yadda faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya zai iya shafar kasafin kudin 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kudurin daftarin kasafin kuɗin 2026 wanda ya kai Naira tiriliyan 58.18, wanda masana tattalin arziki suka nuna damuwa a kansa.

Babbar damuwar da masana suka nuna ita ce yadda gwamnati ta dogara kacokan kan hasashen kasuwar danyen mai wadda ka iya rugujewa cikin kankanin lokaci sakamakon rashin tabbas na tattalin arziki a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ware sama da N1bn don yi wa gidajen Tinubu, Shettima kwaskwarima

An gargadi Tinubu game da kasafin 2026 da ya gabatar wanda ya dogara da danyen mai
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi ga majalisar hadin gwiwa ta tarayya lokacin gabatar da kasafin kudi a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Facebook

Yadda Tinubu ya tsara kasafin kudin 2026

A cikin kasafin 2026 da Tinubu ya gabatar wa majalisar dokokin kasa a 19 ga Disamba, 2025 a Abuja, gwamnati ta kiyasta cewa farashin gangar mai zai tsaya a $64.85, in ji wani rahoton BBC.

Shugaba Bola Tinubu ya kuma shaidawa sanatoci da 'yan majalisar wakilai cewa Najeriya za ta rika samar da ganga miliyan 1.84 na danyen mai a kowace rana.

Haka kuma, Tinubu ya gina kasafin shekarar 2026 ne kan farashin canjin dala a kan ₦1,400, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.

Waɗannan alkaluma su ne ginshiƙan da gwamnati ke sa ran samun kudin shiga na Naira tiriliyan 34.33, wanda hakan ke barin gibin Naira tiriliyan 23.85.

Gwamnatin Tinubu na shirin cike wannan giɓi, wanda ya kai kashi 4.28 na jimillar kudaden shigar ƙasa ta hanyar karɓar sababbin bashi daga gida da waje.

Barazanar da ke fuskantar kasafin kuɗin 2026

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara

Jaridar Leadership ta ce babban ƙalubalen kasafin shi ne yadda farashin danyen mai ya riga ya fara fāɗuwa ƙasa da abin da gwamnati ta kiyasta, inda ya je har kasa da $60 a makon da ya gabata.

Masana na hasashen cewa farashin man na iya ci gaba da fāɗuwa zuwa $50 a shekarar 2027 sakamakon yawan mai a kasuwar duniya daga ƙasashe kamar Amurka, Brazil, da Guyana.

Bugu da ƙari, wani rahoto na DW ya nuna cewa raguwar buƙatar makamashi a manyan ƙasashe kamar China da Turai na iya ƙara raunana farashin.

A ɓangaren cikin gida, samar da danyen mai a Najeriya ya ragu da kashi 5.9 a watan Nuwamban 2025, inda ake samar da ganga miliyan 1.599 kawai a rana, sabanin miliyan 1.84 da aka sanya a matsayin manufa.

Matsalolin tsaro kamar satar ɗanyen mai, fasa bututun mai, da kuma tsufan kayan aiki na ci gaba da dakile yunkurin ƙasar na kai wa ga matakin da take bukata.

Matsalar da Tinubu zai fuskanta a kasafin 2026

An gargadi Tinubu game da yadda faduwar danyen mai zai iya tarwatsa lissafinsa na kasafin 2026
Shugaba Bola Tinubu ya na gabatar da kundin kasasfin kudin Najeriya ga majalisar dokokin tarayya. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Idan har kudin shigar danyen mai ya ragu, manyan ayyukan raya ƙasa da Tinubu ya ware wa Naira tiriliyan 26.08 za su fuskanci babban cikas.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya ware sama da Naira tiriliyan 1 a domin harkokin zabe

Tarihi ya nuna cewa a duk lokacin da gwamnati ba ta sami kuɗin shigar da take fata ba, ayyukan more rayuwa ne ke fara shan wahala. Waɗannan sun haɗa da:

  • Manyan tituna kamar hanyar Legas zuwa Ibadan, hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano, da kuma hanyar East-West Road.
  • Ayyukan layin dogo daga Ibadan zuwa Kano da kuma na Fatakwal zuwa Maiduguri.

Rashin samun isasshen dala daga sayar da mai zai kuma raunana darajar Naira tare da rage kudaden da Najeriya ke ajiyawa a kasashen waje.

Wannan zai tilasta wa gwamnati ƙara karbo bashi, wanda hakan zai ƙara nauyin biyan kudin ruwa a nan gaba, tare da ƙara jefa talakawa cikin mawuyacin hali na hauhawar farashin kaya.

An ware N2.3bn don tsofaffin shugabannin kasa

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsofaffin shugabannin Najeriya daga mulkin soja zuwa na farar hula da mataimakansu sun samu N2.3bn a kasafin 2026.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a cikin kasafin, ya nuna cewa gwamnatinsa za ta biya dukkan hakkoki da alawu alawus na tsofaffin shugabannin kasar.

Tsofaffin shugabanni irinsu Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, Janar Ibrahim Babangida, Janar Yakubu Gowon, da Janar Abdulsalami Abubakar za su amfana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com