Ashe Harin Amurka Ya Kashe Ƴan Ta'adda a Sokoto, Wani Bidiyo Ya Ɓulla daga Baya

Ashe Harin Amurka Ya Kashe Ƴan Ta'adda a Sokoto, Wani Bidiyo Ya Ɓulla daga Baya

  • Wani idiyon da aka yada ya tabbatar da kashe ‘yan ta’adda da lalata maboyarsu a Sokoto, yayin hare-haren sama na Amurka a ƙarshen Disambar 2025
  • Faifan bidiyon ya nuna hare-hare uku, fashewar makamai, gudun ‘yan ta’adda, da lalata motoci, sai dai ba a tantance adadin wadanda aka kashe ba
  • Sojoji sun ce ana ci gaba da tantance barnar harin, yayin da Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da hadin gwiwar Najeriya da Amurka kan yaki da ta’addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - An gano wani bidiyo wanda ya nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama a hare-haren sama da Amurka ta kai a jihar Sokoto.

Rahoton ya bayyana cewa hare-haren sun gudana ne tsakanin ranakun 24 da 25 ga Disamba, 2025, inda aka kai hari kan maboyar ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Sanatan Najeriya ya gina danƙareren gida, talakawa sun masa rubdugu a intanet

An gano bidiyo game da harin Amurka
Shugaba Donald Trump a yayin kamfe. Hoto: Donald J Trump.
Source: Twitter

Sokoto: Bidiyo ya bayyana kan harin Amurka

A bidiyon da Punch ta gano, an ga hare-hare uku daban-daban, tare da wata babbar fashewa bayan harin farko, alamar cewa akwai makamai masu fashewa.

Bidiyon ya kuma nuna wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suna guduwa bayan harin farko da aka kai musu daga sama.

Rahoton ya ce sojoji sun bi sawun wadanda suka gudu, tare da lalata motocinsu da dama yayin ci gaba da aikin soji.

Sai dai ba a iya tantance adadin mutanen da aka kashe ko motocin da aka lalata ba daga bidiyon kadai.

Majiyoyin soji sun ce ana bukatar cikakken binciken barnar yaki domin sanin tasirin hare-haren gaba daya.

An tabbatar da kisan wasu yan bindiga a harin Amurka a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da Amurka ta kai hari. Hoto: Legit.
Source: Original

Sojoji sun ce ana ci gaba da bincike

Daraktan yada labaran tsaro, Manjo-Janar Michael Onoja, ya ce ana ci gaba da tantance bayanan harin.

Yayin da yake magana da ‘yan jarida a Abuja, Onoja ya ce za a sanar da jama’a sakamakon binciken da zarar an kammala.

Kara karanta wannan

Jarumar fim da bidiyon tsiraicinta ya bazu a intanet ta yi magana

Ya jaddada cewa rahotannin sirri sun tabbatar da kasancewar ‘yan ta’adda a wuraren da aka kai hare-haren kafin aiwatar da su.

Trump ya tabbatar da harin Amurka a Sokoto

Tun da farko, Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da kai hare-haren kisa kan ‘yan ISIS a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Daga baya, Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da harin, tana cewa yana cikin hadin gwiwar yaki da ta’addanci tsakanin Najeriya da Amurka.

Sai dai wasu sun yi ikirarin cewa harin bai cimma wani gagarumin buri ba, lamarin da ya haifar da muhawara a sassa daban-daban.

Mazauna Sokoto sun magantu kan harin Amurka

Kun ji cewa kasar Amurka ta tabbatar da kai wani hari kan yan ta'adda a jihar Sokoto a daren jiya Alhamis 25 ga watan Disambar 2025 da ta gabata.

Mazauna kauyen Jabo a Tambuwal a jihar Sokoto sun shiga tsananin fargaba bayan Amurka ta kai harin bama-bamai.

Wani ganau ya ce karar fashewar makaman ta girgiza gidaje, yayin da jami’an tsaro suka garzaya wurin da abin ya watse.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.