Duk da Umarnin Kotu, Likitoci Sun Yi Barazanar Janye Aiki a Asibitocin Gwamnati
- Likitoci na jami'ar Port Harcourt sun bayyana cewa za su shiga yajin aiki a ranar Litinin domin neman gwamnati ta cika alkawurran da ta dauka
- Wannan barazana na zuwa ne duk da umarnin kotun masana'antu da ta dakatar da su daga gudanar da kowane irin yajin aiki a Najeriya
- Likitocin sun koka kan jinkirin biyan albashi da kuma rashin ingantattun kayan aiki a asibitoci wanda hakan ke barazana ga fannin lafiya a kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rivers - Ƙungiyar likitoci ta NARD reshen jami’ar Port Harcourt (Uniport) ta sanar da tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan tsunduma cikin yajin aikin gama-gari na sai-baba-ta-gani.
Wannan na zuwa ne bayan umarnin kotun masana'antu na ranar Juma’a, 9 ga Janairu, 2026, wanda ya haramta wa likitocin shiga yajin aikin da aka shirya farawa ranar Litinin, 12 ga Janairu.

Kara karanta wannan
An cafke jami’in DSS da ake zargi ya tursasa wa budurwa barin Musulunci bayan dirka mata ciki

Source: Twitter
Likitoci na barazanar shiga yajin aiki
A yayin wani taron manema labarai a birnin Port Harcourt, shugabar NARD ta Uniport, Dr. Ezinne Kalu, ta yi magana game da yajin aikin da suke da niyyar shiga, in ji rahoton Channels TV.
Dr. Kalu ta ce likitocin sun janye yajin aikin da suka yi a watan Nuwamban 2025 ne saboda kyakkyawan fatan cewa gwamnatin tarayya za ta aiwatar da yarjejeniyar (MoU) da aka sanya wa hannu.
Sai dai, ta koka da cewa har yanzu gwamnati ba ta nuna gaskiya ba wajen cika buƙatunsu 19, tana mai cewa:
“Mun janye yajin aikinmu a watan Nuwamban bara da yarjejeniyar cewa gwamnati za ta aiwatar da MoU. Abin takaici, har yanzu ba a yi komai ba."
Korafe-korafen likitoci a wajen gwamnati
Binciken da kwamitin E-NEC na NARD ya gudanar, ya nuna cewa akwai matsaloli da dama da suka addabi likitoci, waɗanda suka haɗa da korar likitoci biyar a asibitin koyarwa na Lokoja ba tare da bin ƙa'ida ba, da kuma jinkirin biyan albashi da sauran alawus-alawus.
Haka kuma, likitocin sun bayyana damuwarsu kan taɓarɓarewar kayan aiki da rashin ingantaccen tsarin fansho na musamman ga jami'an lafiya.
Kungiyar NARD ta jaddada cewa kimanin kashi 40 cikin 100 na mambobinsu har yanzu ba su karɓi wasu daga cikin hakkokinsu na aiki ba.

Source: Facebook
Likitoci za su gudanar da zanga zangar lumana
Saboda haka, ƙungiyar ta umurci dukkan mambobinta a asibitoci 91 na gwamnatin tarayya da su janye ayyukansu baki ɗaya daga ƙarfe 12:00 na daren ranar Litinin.
Kazalika, an umurci shugabannin ƙungiyar a faɗin ƙasar da su shirya zanga-zangar lumana idan har gwamnati ta ci gaba da yin kunnen uwar shegu da buƙatunsu.
Wannan dambarwa na barazana ga rayuwar marasa lafiya, yayin da likitocin suka ce ba za su koma bakin aiki ba har sai gwamnati ta nuna alamun gaskiya ta hanyar biyan dukkan bashi da kuma mayar da likitocin da aka kora.
Gwamna ya rufe asibitin kwararru
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Taraba ta ba da umarnin rufe asibitin kwararru dake Jalingo domin ba yan kwangila damar yin gyare-gyare.
Kwamishinan lafiya ya bayyana cewa matakin ya zama dole saboda hadarin muhalli dake tattare da ayyukan gine-ginen da ake gudanarwa.
Sai dai, wani bincike ya nuna cewa marasa lafiya da ke wankin koda sun shiga tashin hankali saboda rashin wurin da za su je wankin
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

