Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu Ya Dauka bayan Alaka Ta Sake Tsami tsakanin Wike da Fubara

Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu Ya Dauka bayan Alaka Ta Sake Tsami tsakanin Wike da Fubara

  • Rikicin siyasar jihar Rivers ya sake daukar zafi, inda har ya kai ga an fara yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa
  • Sake barkewar rikicin na zuwa ne watanni uku bayan Shugaba Bola Tinubu ya janye dokar ta bacin da ya kakaba na watanni jihar
  • Alamu sun nuna cewa a wannan karon ma, Shugaba Bola Tinubu ya sake shiga tsakani don warware rikicin siyasar jihar mai arzikin mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Akwai alamun da ke nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani a rikicin da ke gudana tsakanin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

A cewar wata majiya mai matukar sahihanci, Shugaba Tinubu ya gayyaci Wike domin tattaunawa kan rikicin Rivers.

Tinubu ya shiga tsakani kan rikicin siyasar jihar Rivers
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Ezenwo Wike Hoto: @GovWike, @SimFubaraKSC, @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce majiyar, wadda ke kusa da shugaban kasa, ta shaida mata cewa za a gudanar da taron ne a kasar waje.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi albishir ga 'yan Najeriya game da tsadar kayan abinci a 2026

Gwamna Simi Fubara ya bar Najeriya

Haka kuma, an gano cewa Gwamna Fubara ya bar kasar nan a ranar Alhamis, 8 ga watan Janairun 2026 da nufin ganawa da Shugaba Tinubu a Faransa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin ‘yan majalisar dokokin jihar Rivers, waɗanda ake cewa suna biyayya ga Wike, sun kaddamar da sabon yunkurin tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, daga mukamansu.

Wane mataki Shugaba Tinubu ya dauka?

Da take magana kan wannan sabon shirin tsige gwamnan, majiyar ta bayyana cewa shugaban kasa ya riga ya shiga tsakani.

“Dole ne shugaban kasa ya fahimci hatsarin da ke tattare da abin da Wike ke yi. Na san cewa ya riga ya gayyace shi zuwa wata ganawa a Dubai. Ka san Shugaban ƙasa a halin yanzu yana wajen kasar nan."
"Idan ba wani sauyi aka samu ba, ana sa ran za su gana a kasashen waje. Wike ba zai iya tsige Fubara ba, shugaban kasa zai taka masa birki."

Kara karanta wannan

Siyasar Rivers: Dalilan da suka jawo sabon rikici tsakanin Fubara da Wike

- Wata majiya

An ce Wike bai mutunta Shugaba Tinubu

Majiyar ta bayyana ayyukan Ministan na Abuja a matsayin rashin girmamawa ga shugaban kasa, tana mai gargaɗi cewa idan ba a yi hattara ba, hakan na iya tursasa matasan Ijaw su koma fasa bututun mai.

“Abin da ke faruwa rashin mutunta shugaban kasa ne kai tsaye daga Wike, kuma hakan ya saɓa wa muradun ƙasa."
"Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa aka ayyana dokar ta-baci a Rivers a watan Maris na shekarar da ta gabata shi ne fargabar barkewar rashin bin doka da oda da kuma illar hakan ga samar da man fetur."
“Idan aka ce ana son tsige ɗan Ijaw na farko da ya zama gwamnan jihar, shin hakan ba saƙo ba ne na tura mutanen Ijaw su koma fasa bututun mai? Hakan zai yi mummunan tasiri ga tattalin arziki, kuma shugaban kasa ba zai bari hakan ta faru ba.”

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara shirin tsige gwamna Fubara bayan sabon rikici da Wike

- Wata majiya

Batun ganawar Tinubu da Wike

Wani babban mataimaki ga shugaban kasa ya ce bai san komai ba game da ganawar da ake cewa za a yi da Wike, yana mai kara da cewa a halin yanzu Tinubu yana Faransa, daga nan kuma zai wuce birnin Abu Dhabi a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Majiyar ta lura cewa Ministan Abuja ba shi da wata muhimmin aiki a UAE, face dai idan yana da shirin ganawa da shugaban kasa.

“Sai dai Wike ko mataimakansa ne kawai za su iya tabbatar da ko akwai wata ganawa da aka shirya tsakaninsa da shugaban kasa."
“Lokacin da Fubara ya koma APC, ya gana da Tinubu wanda ya amince da matakin. Shugaban kasa ya kuma jaddada cewa gwamnonin jihohi su ne shugabannin jam’iyya a jihohinsu.”

- Wata majiya

Majiyoyin sun ce Nyesom Wike zai gana da Shugaba Bola Tinubu
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Source: Twitter

Wani babban jami’i a ɓangaren gudanarwa na sakatariyar APC ta kasa ya ce ana ci gaba da tattaunawa kan yadda shugabannin jam’iyyar na kasa za su gana da Shugaba Tinubu da zarar ya dawo kasar nan.

Kara karanta wannan

Malami ya fadi manyan Najeriya 3 da za su tilasta wa Atiku janye wa Jonathan

Ya ce shugabannin APC ba su ji daɗin abin da Wike ke yi ba.

Me makusantan Wike suka ce?

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Ministan, Lere Olayinka, bai yi nasara ba, domin bai ɗauki kira ko amsa sakonnin da aka tura masa ba.

Sai dai wata ta kusa da Ministan, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce zai koma birnin Abuja ranar Lahadi.

Da aka tambaye ta game da batun ganawar da shugaban kasa, sai ta ce:

“Mu jira lokacin ya yi. Ba sai mun yi gaggawa ba.”

Ta kuma wanke Ministan daga hannu a shirin tsige Fubara, tana mai cewa ‘yan majalisar dokokin jihar Rivers ne ke jagorantar wannan yunkuri.

Abin da zai ceci Gwamna Fubara a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Rivers.

Ayodele Fayose ya bayyana cewa ya bayyana cewa azumi da yawaita rokon Allah ne kadai za su iya ceton Gwamna Siminalayi Fubara.

Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya shawarci Fubara da ya yi sulhu da tsohon ubangidansa kuma magabacinsa, Nyesom Wike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng