Yajin Aiki: Kotu Ta ba da Umarnin Wucin Gadi a Shari'ar Gwamnati da Likitoci
- Babbar kotun masana'antu dake Abuja ta dakatar da kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki daga shiga yajin aiki a mako mai zuwa
- Mai shari'a E. D. Subilim ya bayar da wannan umarni ne bayan gwamnatin tarayya ta shigar da korafi domin hana likitocin janye ayyukansu
- Likitocin sun yi barazanar fara yajin aikin ne saboda zargin rashin gaskiyar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a bara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babbar Kotun Masana'antu da ke Abuja ta yanke wani hukuncin wucin gadi a ranar Juma’a, 9 ga Janairu, 2026, na dakatar da likitoci daga shiga yajin aiki.
Wannan hukunci ya hana likitocin da ke neman kwarewar aiki (NARD) shiga yajin aikin da suka shirya farawa daga ƙarfe 12:00 na daren ranar Litinin, 12 ga Janairu, 2026.

Source: Getty Images
Kotu ta saurari karar gwamnati da likitoci
Mai shari'a E. D. Subilim ne ya yanke wannan hukuncin biyo bayan ƙarar da gwamnatin tarayya da babban lauyan kasa suka shigar, in ji rahoton The Nation.
Wannan takaddama ta samo asali ne bayan da likitocin asibitin mahaukata na Aro da ke Abeokuta, da sauran rassan ƙungiyar ta NARD, suka bayyana aniyar tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani.
Likitocin sun yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta nuna “rashin gaskiya da halin ko-in-kula” wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a baya.
Kotu ta hana likitoci shiga yajin aiki
Idan za a iya tunawa, Legit Hausa ta rahoto cewa likitocin sun dakatar da wani yajin aiki na kwanaki 29 a watan Nuwamban 2025 bayan alkawuran da gwamnati ta ɗauka, waɗanda yanzu suke zargin ba a cika su ba.
A cikin hukuncin da ya yanke, Mai shari'a Subilim ya haramta wa ƙungiyar NARD, shugabanninta, da dukkan mambobinta “kira, tsarawa, halarta, ko tsunduma cikin kowane irin yajin aiki, jinkirta aiki, ko zanga-zanga a wuraren aiki” har sai an kammala shari'ar gaba daya.
Kotun ta bayyana cewa:
“An ba da umarnin dakatar da waɗanda ake ƙara, mambobinsu, ko wakilansu daga ɗaukar kowane mataki na shirya yajin aiki daga 12 ga Janairu, 2026, har sai an saurari ƙudurin da ke gaban kotu.”

Source: Twitter
Abin da likitoci za su iya yi yanzu
Wannan umarni zai ci gaba da aiki har zuwa ranar 21 ga Janairu, 2026, lokacin da kotun za ta saurari hujjojin ɓangarorin biyu, in ji rahoton The Punch.
Gwamnati ta samu umarnin isar da takardun kotun ga likitocin a cikin kwanaki bakwai, yayin da su kuma likitocin ke da damar garzayawa kotun don neman soke wannan umarni idan suna da hujjoji masu ƙarfi.
Wannan mataki na kotu ya sa an samu annuri a fannin lafiyar kasar, inda ake fargabar durƙushewar asibitocin gwamnati idan har likitocin suka janye aiki.
NARD: Likitoci za su shiga yajin aiki
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Kungiyar likitoci ta NARD ta sanar da shawarar da ta ɗauka na komawa yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar nan.
Likitocin sun ce daga ranar 12 ga watan Janairun shekarar da muke ciki, mambobin kungiyar za su janye aiki daga kowanne asibiti na fadin Najeriya.
NARD ta kuma ba da umarnin gudanar da zanga-zangar lumana a dukkan asibitoci 91 da ke ƙarƙashin ƙungiyar a faɗin ƙasar nan don nuna fushinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


