Za a Sha Ayyuka: Majalisa Ta Amince Gwamna Ya Kashe Naira Tiriliyan 4.4 a 2026
- Majalisar dokokin jihar Legas ta amince da kasafin kudi na Naira tiriliyan hudu da digo hudu domin gudanar da ayyukan raya kasa
- Babban burin wannan kasafin shi ne kawar da talauci da kuma gina Legas da za ta amfani dukkan mazaunanta, in ji Gwamna Sanwo-Olu
- Shugaban majalisa Mudashiru Obasa ya umarci a mika kasafin kudin ga gwamna domin sanya hannu yadda za a fara aiwatar da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Majalisar dokokin jihar Legas ta amince da jimillar Naira tiriliyan 4.44 a matsayin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026.
Shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, ne ya sanar da amincewa da wannan kudurin dokar kasafin yayin zaman majalisar na ranar Alhamis, 8 ga Janairu, 2026.

Source: Twitter
Majalisar Legas ta amince da kasafin 2026
Wannan kasafin kuɗin, wanda aka yi wa laƙabi da "Kasafin Raba Arziƙi", ya haura tiriliyan 4.237 da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gabatar wa majalisar tun da fari a watan Nuwamban 2025, in ji rahoton Punch.
Shugaban kwamitin tsare-tsaren tattalin arziki da kasafin kuɗi, Olumoh Sa’ad, ya bayyana cewa daga cikin jimillar N4,444,509,776,438 da aka amince da su, an ware Naira tiriliyan 2.106 domin ayyukan yau da kullum, yayin da aka ware Naira tiriliyan 2.337 domin ayyukan raya ƙasa.
Bayan amincewa da dokar, Obasa ya umarci magatakardan majalisar, Olalekan Onafeko, da ya mika kwafin kasafin kuɗin ga Gwamna Sanwo-Olu domin ya sanya hannu.
Ayyukan da za a yi cikin kasafin Legas
Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa babban burin wannan kasafin kuɗi shi ne kawar da talauci da kuma gina jihar Legas da za ta amfani dukkan mazaunanta.
Kasafin kuɗin ya ginu ne a kan ginshiƙai huɗu: mayar da hankali ga buƙatun ɗan Adam da samar da ingantattun ababen more rayuwa.
Sauran bangarorin biyu su ne; bunƙasa tattalin arziƙi, da kuma shugabanci na gari, waɗanda duka suke tafiya daidai da tsarin T.H.E.M.E.S+ na gwamnatin jihar.

Source: Facebook
'Yan Legas za su mori kasafin kudin 2026
A cikin shekarar 2026, gwamnatin jihar ta yi alƙawarin faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi, ƙarfafa fannin lafiya, da kuma samar da gidaje masu sauƙin kuɗi, inji wata sanarwa a shafin gwamnatin Legas.
Haka kuma, gwamnan ya nanata cewa za a mayar da hankali wajen kammala manyan ayyuka da kuma amfani da fasahar zamani domin inganta zirga-zirga da ayyukan gwamnati.
Har ila yau, za a ga gagarumin sauyi a fannin gyaran birane da tsarin kwashe shara domin magance matsalar ambaliyar ruwa da ke addabar jihar.
Sanwo Olu ya ba Tinubu kwarin gwiwa
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya ce yan Najeriya za su saka wa Bola Tinubu da kuri'unsu a zaben 2027.
Mai girma gwamnan ya ce matakan da Tinubu ya dauka na farfado da Najeriya kadai sun isa su sa 'yan Najeriya kara zabensa a karo na biyu.
Sanwo-Olu ya kuma bayyana yadda APC ta samu karin gwamnoni daga 20 zuwa 29, yana mai cewa duka sun amince su marawa Tinubu baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

