An Taso Ministan Tinubu a Gaba, an Roki Shugaban Kasa Ya Fatattake Shi

An Taso Ministan Tinubu a Gaba, an Roki Shugaban Kasa Ya Fatattake Shi

  • Kungiyar NADECO USA ta tura bukata ta musamman ga Shugaba Bola Tinubu game da Ministan Abuja, Nyesom Wike
  • Ta roki shugaban da ya dauki matakin gaggawa kan Wike domin kawo ƙarshen rikicin siyasa a Jihar Rivers
  • NADECO USA ta ce Wike ne tushen rikicin Rivers, tana gargadin cewa idan shugaban ƙasa bai ɗauki mataki ba, rikicin zai ƙara muni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar National Democratic Coalition (NADECO), reshen Amurka, ta roki Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin gaggawa kan ministansa.

Kungiyar ta bukaci Tinubu da ya sallami Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike daga mukaminsa.

An roki Tinubu ya sallami Wike daga mukaminsa
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Nyesom Wike, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: UGC

Rahoton Vanguard ya ce kungiyar ta bukaci haka ne a matsayin mataki na kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya daɗe yana addabar Jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Tofa: Jagororin APC sun taso Tinubu a gaba, suna so ya tsige ministan Abuja

An roki Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Arewa

Kungiyar mai rajin dimokuraɗiyya ta kuma buƙaci Shugaban Ƙasa da ya ayyana dokar ta-ɓaci ta tsawon watanni shida a wasu sassan Arewacin Najeriya.

Ta yi gargadin cewa ba za a iya gudanar da sahihin zaɓe ba a yankunan da ‘yan ta’adda ke iko da su gabanin zaɓen 2027.

Da yake jawabi, Shugaban NADECO USA, Dakta Lloyd Ukwu, ya zargi Nyesom Wike da kasancewa jigon rikicin Rivers, yana mai cewa ba za a samu zaman lafiya ba matuƙar ba a hukunta ministan ba.

A cewarsa, sallamar Wike daga muƙaminsa za ta nuna cewa Shugaba Tinubu ba ya goyon bayan tasirin da ake zargin ministan na yi fiye da kima a harkokin siyasar jihar Rivers.

Ya ƙara da cewa fara shirin tsige gwamnan Rivers a lokacin da Shugaban Ƙasa ke ƙasashen waje ya ƙara nuna buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa, cewar Daily Post.

Ukwu ya ce:

“Babbar matsalar da ake fuskanta a Rivers a yau, dangane da wannan rikici, ita ce Ministan Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisar Rivers ta lissafo zunuban Fubara 11 yayin take shirin tsige shi

Mutanen Rivers sun san inda matsalar take. Dole ne Shugaban Ƙasa ya kira shi ya ja masa kunne. Wike ma’aikacinsa ne.
“Idan Rivers ta rufta, za mu ɗauki Shugaban Ƙasa a matsayin mai laifi idan bai ɗauki mataki ba.”
Kungiya ta roki Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Arewa
Shugaba Bola Tinubu yana sauraron jawabi yayin taro. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

'Matsalolin Arewa na barazana ga dimukradiyya'

Dangane da matsalar tsaro a ƙasa, shugaban NADECO USA ya bayyana cewa dimokuraɗiyyar Najeriya na fuskantar barazana mai tsanani sakamakon taɓarɓarewar tsaro a Arewa.

Ya ce:

“Ta ya ya kuma a ina mutane za su yi zaɓe idan ‘yan ta’adda ne ke iko da al’ummominsu? Muna magana kan zaɓen 2027 alhali mun kasa kare rayuka da dukiyoyin jama’a.”

APC ta bukaci Wike ya yi murabus

Kun ji cewa sakataren jam'iyyar APC na kasa, Ajibola Basiru ya maida raddi mai zafi ga Ministan Harkokin birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Basiru ya bukaci Wike ya ajiye mukaminsa na minista a gwamnatin APC domin ba zai yiwu su zuba masa ido yana haddasa rikici a jam'iyya ba.

Wannan na zuwa ne bayan Wike ya gargadi Basiru da ya tsame kansa daga harkokin siyasar jihar Rivers wanda ta dauki zafi tun daga 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.