Rigima Ta Kara Zafi, Sakataren APC na Kasa Ya Nemi Ministan Tinubu Ya Yi Murabus
- Sakataren jam'iyyar APC na kasa, Ajibola Basiru ya maida raddi mai zafi ga Ministan Harkokin birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike
- Basiru ya bukaci Wike ya ajiye mukaminsa na minista a gwamnatin APC domin ba zai yiwu su zuba masa ido yana haddasa rikici a jam'iyya ba
- Wannan na zuwa ne bayan Wike ya gargadi Basiru da ya tsame kansa daga harkokin siyasar jihar Ribas idan ba haka ba ta kona shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rikicin da ya barke tsakanin Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike da sakataren APC na kasa, Ajibola Basiru ya kara zafi a yau Litinin.
Basiru ya bukaci Wike ya yi murabus daga mukaminsa na Ministan Abuja tare da mayar da hankali kan abin da ya kira “ciwon damuwa da siyasar Jihar Ribas."

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta tattaro cewa sakataren APC, Ajibola Basiru ya fadi haka ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.
Ya jaddada cewa dole duka mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na APC ta kasa su girmama gwamnonin da ke kan mulki tare da amincewa da su a matsayin jagororin jam’iyyar a jihohinsu.
Gargadin da Wike ya yi wa sakataren APC
Tun da farko, Wike ya gargadi sakataren jam’iyyar APC na kasa da ya nisanta kansa daga harkokin siyasa siyasar Jihar Ribas ko kuma ta kona shi, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Minista Wike ya yi wannan gargadi ne bayan Basiru ya ja kunnen mataimakin shugaban APC (Kudu maso Kudu) kan rashin da'ar da ya yi wa Gwamna Siminalayi Fubara na Ribas.
Basiru, a cikin wata sanarwa mai zafi da ya fitar don martani, ya ce hankalinsa ya kai kan abin da ya kira “kalaman cin mutunci da Ministan Abuja ya yi a kaina da kuma ofishina na sakataren APC."
Sakataren APC ya maida martani ga Wike
Ya nuna matukar mamakinsa kan yadda Wike ya nemi keta mutuncinsa saboda kawai ya fadi matsayarsa game da mutunta gwamnoni ba tare da la'akari da banbancin jam'iyya ba.
Ya kuma bayyana mamakinsa cewa magana mai sauki da ya yi cikin ruwan sanyi ta iya haifar da irin wadannan kalamai marasa da’a daga bakin wani mamba a Majalisar Zartarwa ta Tarayya.
Basiru ya ce bai dace ba Wike ya ci gaba da zama a cikin majalisar ministocin gwamnatin APC ba alhali yana haddasa rikice-rikice a cikin jam’iyyar.

Source: Twitter
Basiru ya nemi Wike ya yi murabus
Sakataren APC ya ce:
“Ba zai yiwu mutumin ya kassnce a cikin Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta gwamnatin APC, amma yana haddasa rikici a jam’iyyar ko tsarinta a kowane mataki ta hanyar amfani da karfin mukamin da aka ba shi ba.”
Ya kara da cewa, “abin da ya dace shi ne ya yi murabus daga mukaminsa na Minista.”
Sakataren APC na kasa ya jaddada cewa Wike ba shi da hurumin shiga harkokin cikin gidan jam’iyyar APC, yana mai cewa a fili:
“Bayananmu sun nuna cewa Minista Nyesom Wike ba mamba ba ne na jam’iyyarmu ta APC, don haka ba shi da ikon tsoma baki cikin harkokin jam’iyyarmu," in ji Basiru.
Wike ya hango karshensa a siyasance
A wani labarin, kun ji cewa Nyesom Wike ya ce siyasarsa na iya mutuwa murus idan Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya yi tazarce a 2027.
Duk da bai ambaci sunan gwamnan kai tsaye ba, Ministan ya bayyana cewa tuni suka yanke shawara mai tsauri game da zaben gwamnan Ribas na 2027.
Wike ya zargi gwamnan da karya sharuddan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma kafin a dage dokar ta-baci a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


