Ana Murna Dala Ta Karye, Ƴan Kasuwa Sun Sauke Farashin Gas din Girki a Najeriya
- 'Yan kasuwa sun fara sauke farashin iskar gas na girki ya fara saukowa bayan an shafe watanni ana fuskantar karancinsa a kasuwanni
- Rahoto ya nuna cewa kasuwar ta fara daidaita sakamakon karuwar gas din daga manyan dillalai zuwa kananan 'yan kasuwa na anguwanni
- 'Yan Najeriya na fatan ganin farashin kowanne kilogiram daya na gas din ya koma kasa da N1000 domin karfafa amfani a kan gawaki ko icce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Akwai alamun samun sauƙi ga masu amfani da iskar gas din girki (LPG) yayin da gas din ya fara wadata a kasuwanni.
A halin yanzu, ana sayar da kilogiram ɗaya na gas din girki tsakanin N1,000 zuwa N1,400, ya danganta da yanki da kuma mai sayarwa.

Source: Getty Images
An sauke farashin gas din girki
Binciken kasuwa da jaridar Punch ta yi ya nuna cewa an fi samun gas din girki a ƙarshen 2025, idan aka yi la'akari da ƙarancinsa da aka samu Satumba da Oktobar bara.
Wannan sauƙin farashin ya biyo bayan tsananin tsadar da aka fuskanta a baya lokacin da aka samu saɓani tsakanin matatar man Dangote da ƙungiyar ma’aikatan mai ta PENGASSAN, wanda ya kai ga rufe wuraren samar da gas.
Masu amfani da gas a jihohin Legas, Ogun, da Oyo sun tabbatar da cewa suna sayen kilogiram ɗaya a kan farashin N1,050 zuwa N1,400.
Binciken ya kuma nuna cewa wasu manyan dillalan ma suna sayar da shi akan N900 kai tsaye ga masu buƙata.
Ana ganin hakan babban ci gaba ne ga iyalai da dama waɗanda tuni suka suka koma amfani da gawayi ko itace a lokacin da farashin gas din ya yi tashin gwauron zabi.
Farashin da dillalai ke sayo gas din girki
Shugaban ƙungiyar masu sayar da iskar gas din girki (LPGAR) na ƙasa, Ayobami Olarinoye, ya bayyana cewa yanayin kasuwar ya fara daidaita yanzu.
A cewar Ayobami Olarinoye, masu sayarwa a shagunan kan titi suna sayarwa tsakanin N1,300 zuwa N1,400, yayin da a manyan kamfanonin gas ke sayarwa kasa da saboda sauƙin sufuri da tsarin kasuwancinsu.
Ya ƙara da cewa su kansu dillalai suna sayo gas ɗin ne akan N960 zuwa N1,050 a hannun manyan kamfanoni, wanda hakan ke nuna cewa riba kaɗan suke ɗora wa idan aka yi la'akari da kuɗin sufuri da hayar shaguna.

Source: Getty Images
Ana fatan kilo na gas ya koma N1000
Duk da wannan ci gaba, ’yan Najeriya da dama na fatan ganin farashin ya faɗo ƙasa da N1,000 kan kowane kilogiram ɗaya a wannan sabuwar shekara domin sauƙaƙa wa talakawa.
Idan za a iya tunawa, farashin gas ya taɓa haura N2,000 a wasu wuraren a lokacin yajin aikin da aka yi a bara.
Matatar man Dangote ta taɓa yin alƙawarin rage farashin gas ta hanyar sayarwa ga jama'a kai tsaye a nan gaba, matakin da masana ke ganin zai iya karya farashin gaba ɗaya idan aka fara aiwatar da shi.
Dalar Amurka ta karye a kasuwa
A wani labari, mun ruwaito cewa, Naira ta kara samun karfi tare da zuwa matsayi mafi girma da ba a taɓa gani ba na N1,418.26/$1 a kasuwar canjin kuɗi ta gwamnati.
Bayanai daga Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa Naira ta shigo shekarar 2026 ne da ƙarfinta, inda a ranar Juma’a ta kai N1,430.84/$1.
Rahoton ya nuna cewa Naira ta tashi zuwa N1,429.30/$1 a ranar Litinin, sannan a ranar Talata, ta lula zuwa N1,419.06/$1, wanda ke wakiltar ƙaruwar kashi 0.72.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

