Bayan Sokoto, An Fadawa Trump Jihar da Ya Kamata Ya Kai Sabon Hari a Najeriya

Bayan Sokoto, An Fadawa Trump Jihar da Ya Kamata Ya Kai Sabon Hari a Najeriya

  • Tsohon ministan shari'a, Michael Aondoakaa ya bukaci gwamnatin Amurka ta kawo hari jihar Benue kamar yadda ta kai hari Sokoto
  • Michael Aondoakaa ya bayyana cewa yan bindiga sun mamaye kananan hukumomi da yawa suna suke kashe mutane da kwace gonakinsu
  • Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayyar ya bayyana muhimmancin harin Amurka a Benue tare da yin magana kan takarar gwamnansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Tsohon Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Michael Aondoakaa, ya yi kira ga gwamnatin Amurka da ta faɗaɗa hare-harenta a Najeriya.

Michael Aondoakaa ya nunawa Shugaba Donald Trump bukatar da ke da akwai ta turo jiragen yakin sojojin saman Amurka zuwa jihar Benue domin kakkabe ’yan ta’adda.

An bukaci Trump ya kawo harin sama a jihar Benue da ke Arewacin Najeriya.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya na jawabi a wajen wani taro. @realDonaldTrump
Source: Getty Images

An bukaci Amurka ta kawo hari Benue

Aondoakaa ya yi wannan kiran ne a daren Juma'a yayin wata liyafar cin abincin dare da shugabannin jam’iyyun APC da PDP a Makurdi, a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Jerin kungiyoyin 'yan ta'adda 8 da Amurka ta fi damuwa da ayyukansu a Najeriya da Afirka

Tsohon ministan shari'ar, wanda ya rike mukamin a lokacin mulkin marigayi Umaru Musa Yar'Adua, ya bayyana cewa jihar ta dade da bukatar irin wannan harin saboda matsalar tsaro.

Wannan kiran na zuwa ne biyo bayan hare-haren bam da jiragen yaƙin Amurka suka kai kan sansanonin ’yan ta’adda masu alaƙa da ƙungiyar ISIS a dajin Bauni da ke jihar Sokoto a ranar Kirsimeti.

Aondoakaa ya bayyana cewa, akwai buƙatar irin waɗannan hare-haren a Benue domin ’yan ta’adda sun mamaye ƙananan hukumomi da dama a jihar, inda suke fake da sunan makiyaya suna karkashe mutane tare da ƙwace musu filaye.

Siyasar 2027 da kalubalen tsaro a Benue

Tsohon ministan, wanda a yanzu yake neman takarar gwamnan Benue a zaɓen shekarar 2027, ya soki gwamnatin jihar kan abin da ya kira rashin nuna damuwa ga matsalar tsaro.

Ya ambaci kisan kiyashin da aka yi a yankin Yelwata, inda aka kashe kusan mutum 200 a rana guda, a matsayin hujjar buƙatar agajin soja na ƙasa da ƙasa.

Michael Aondoakaa ya yi alƙawarin cewa idan har aka zaɓe shi a matsayin gwamna, samar da tsaro zai zama babban fifikon gwamnatinsa, in ji rahoton Arise News.

Kara karanta wannan

Albishir da Gwamna Radda ya yi ga al'ummar Katsina game da ta'addanci

Michael Aondoakaa ya ce akwai buƙatar irin waɗannan hare-haren Amurka a jihar Benue saboda matsalar ’yan ta’adda da ta addabi jihar.
Taswirar jihar Benue da ke Arewacin Najeriya, inda ake son Amurka ta farmaka. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tsohon gwamna ya roki 'yan siyasar Benue

A yayin taron, tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom, ya jinjina wa ƙoƙarin Aondoakaa, inda ya bayyana shi a matsayin jagora mai kwarewa da mutunci.

Ortom ya yi kira da a haɗa kai tsakanin dukkan jam’iyyun siyasa domin fitar da jihar Benue daga kangin rashin tsaro da rashin ci gaba, in ji rahoton wata jaridar intanet, Benue Today.

Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, kan ƙoƙarin da suke yi na dinke ɓarakar siyasa da tsaro a ƙasar.

'Yan bindiga sun mamaye gari guda a Benue

A wani labari, mun ruwaito cewa, makiyaya dauke da miyagun makamai sun mamaye gonaki da gidajen mutane a garin Dyom, da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benue.

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun kafa sansanoni a ciki da kewayen garin, suna kuma boyewa cikin gonaki idan jami’an tsaro ko ‘yan sa kai na Anyam Nyor suka je yankin.

Da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Benue, DSP Edem Edet, ta ce ba ta samu cikakken rahoto kan lamarin ba tukuna, amma za ta bibiyi lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com