Jirgin Saman Sojoji Ya Yi Hatsari a Kokarin Yaki da ’Yan Ta’adda a Niger
- Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin yaki marar matuƙi na Rundunar Sojojin Sama ya faɗi a dajin jihar Niger
- Hatsarin ya faru ƙasa da sa’o’i 48 bayan ’yan ta’adda sun kashe manoma biyu tare da ƙona gidaje 13 a jihar
- Rundunar Sojojin Sama ta ce babu asarar rayuka, kuma ayyukan yaƙi da ta’addanci na ci gaba ba tare da tangarɗa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kwantagora, Niger - Jirgin sama marar matuƙi na Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) ya yi hatsari a wani daji a jihar Niger.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an samu hatsarin ne a dajin Zangata da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora, a Jihar Niger.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya tara 'yan Kwankwasiyya a;hali Abba na shirin hada kai da Ganduje a APC

Source: Getty Images
Yadda 'yan bindiga suka farmaki mutane a Niger
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a 2 ga watan Janairun 2026 da yamma, jim kaɗan bayan hare-haren ’yan ta’adda a ƙauyukan Goro da Gebe na Ƙaramar Hukumar Agwara, cewar Aminiya.
Yayin harin, an ce maharan sun kashe manoma biyu tare da ƙona aƙalla gidaje 13 wanda ya tayar da hankulan al'ummar yankin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ƙauyukan da aka kai harin na kan iyaka tsakanin Borgu da Agwara, kuma ana zargin maharan sun tsere zuwa Jihar Neja ne daga Kwara bayan matsin lambar da sojoji suka musu.
Wani mazaunin Kontagora, Zakari Adamu, ya ce jami’an tsaro ciki har da sojoji da ’yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru, amma a lokacin ba a tabbatar da irin ɓarnar da jirgin ya yi ko asarar rayuka ba.

Source: Original
Martanin rundunar sojoji kan lamarin
Rundunar Sojojin ta tabbatar da faruwar hatsarin, inda ta bayyana cewa jirgin ya rasa sadarwa da cibiyar kulawa bayan an tura shi domin ci gaba da ayyukan yaƙi da ta’addanci.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Air Commodore Iya Komodo Ehimen Ejodame, ya fitar, rundunar ta ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon hatsarin, cewar Sahara Reporters.
Ejodame ya ƙara da cewa an ɗauki matakan gaggawa domin gano jirgin tare da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro da kuma aikin ceto.
Ya bayyana cewa tuni aka gano jirgin, kuma ƙwararrun injiniyoyi sun fara tantance dalilin hatsarin tare da aikin dawo da shi bisa ƙa’idojin tsaro da aiki.
Rundunar Sojojin Sama ta jaddada cewa duk da faruwar hatsarin, ayyukan tsaro da yaƙi da ta’addanci na ci gaba a dukkan yankunan da ake fama da matsalolin tsaro a ƙasar nan.
Jirgin sojoji ya yi hatsari a Niger
A baya, kun ji cewa wani jirgin sama na rundunar sojojin Najeriya ya gamu da hatsari a kusa da Karabonde, cikin Karamar Hukumar Borgu ta jihar Niger.
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa matukan jirgin sun samu nasarar fita lafiya tun kafin jirgin ya kife.
Rundunar sojojin sama ba ta ce komai ba kawo yammacin na yau amma an fara yada bidiyoyin yadda jirgin ya kama da wuta bayan hatsarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

