Kudin Babura: EFCC Ta Gurfanar da Jami'in Gwamnati kan Zargin Handame N5.79bn

Kudin Babura: EFCC Ta Gurfanar da Jami'in Gwamnati kan Zargin Handame N5.79bn

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da kwamishinan kudin Bauchi, Yakubu Adamu bisa zargin ya karkatar da fiye da Naira biliyan biyar
  • Ana zargin ya karkatar da biliyoyin kudin da aka fitar don sayen wasu baburan gwamnati kafin a nada shi mukamin kwamishina
  • Lauyan EFCC, Samuel I. Chime, ya yi bayani game da tuhume tuhumen da ake yi wa kwamishinan da yadda ya aikata lafin a 2022

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da kwamishinan kuɗi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu, a gaban babbar kotun tarayya da ke Maitama, Abuja.

EFCC ta gufarnar da kwamishinan tare da wasu a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite a ranar Talata, 30 ga watan Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Bam a masallaci: Wanda ake zargi ya fadi makudan kudi da aka ba shi a Borno

EFCC ta gurfanar da kwamishinan kudi na jihar Bauchi bisa zargin karkatar da kudade.
Kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu a lokacin da EFCC ke kokarin shigar da shi kotu a Abuja. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

EFCC ta gurfanar da kwamishinan kudin Bauchi

A wata sanarwa da aka wallafa a shafin EFCC na X, hukumar na tuhumar Yakubu tare da kamfanin Ayab Agro Products and Freight kan zarge-zarge guda shida.

Zarge zargen da ake yi wa kwamishinan kudi da kamfanin sun shafi karkatarwa da halatta kuɗin haram da jimillarsu ta kai Naira biliyan 5.79.

A cewar EFCC, waɗanda ake tuhumar sun aikata laifuffukan da suka saɓa wa sassa na dokar hana halatta kuɗin haram ta shekarar 2022.

Bayan karanta tuhume-tuhumen, Yakubu Adamu ya bayyana cewa ba shi da laifi a dukkan zarge zargen da ke kunshe cikin kundin tuhume-tuhumen.

Lauyan mai ƙara, Samuel I. Chime, ya buƙaci kotun ta ci gaba da shari'ar bayan an kammala karanta wa waɗanda ake tuhume-tuhumen da ake yi masu.

EFCC: Zargin satar kuɗin sayen babura

Ɗaya daga cikin manyan tuhume-tuhumen ya nuna cewa Yakubu Adamu, ya hada baki da wasu mutane biyu da a yanzu ake nemansu ruwa a jallo wajen aikata laifi.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi umarni a kwace N1.1bn da ake zargin na da alaka da gwamnatin Kano

An ce Yakubu da mutanen biyu da ake nema sun hada baki, sun karkatar da kudi a lokacin da yake matsayin manajan bankin Polaris reshen jihar Bauchi.

EFCC ta ce ana zarginsu da karkatar da Naira biliyan 4.65 waɗanda bankin Polaris ya saki da sunan za a sayo wa gwamnatin Bauchi babura ta hanyar kamfanin Emmanuel Asomugha General Enterprises, amma bincike ya nuna cewa ba a taɓa sayo baburan ba.

Kwamishinan kudi da EFCC ta gurfanar a kotu ya ce bai aikata zambar fiye da N5bn ba.
Harabar babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja. Hoto: @FederalHigh
Source: UGC

EFCC: Yadda kwamishina ya karkatar da N976m

Haka kuma, ana tuhumar Yakubu Adamu da amfani tare da mallakar wasu Naira miliyan 976 waɗanda aka tura zuwa asusun kamfanin I.S. Makayye Investment Resources Limited.

Kamar yadda lauyan EFCC ya karanta bayanan tuhumar, wanda ake zargin ya rarraba Naira miliyan 976 ga mutane da kamfanoni daban-daban.

EFCC ta bayyana cewa waɗanda ake tuhuma sun san cewa waɗannan kuɗaɗen an same su ta hanyar haram, wadanda aka karkatar daga tallafin banki.

Kotun za ta ci gaba da sauraron shari'ar domin yanke shawara kan neman belin kwamishinan, kamar yadda sanarwar EFCC ta nuna.

EFCC ta kwato N42.5m daga ma'aikaciyar banki

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta cafke fiye da mutane 3,000 a Kano, kwamishina ya yi bayani

A wani labari, mun ruwaito cewa, EFCC ta mayar wa wata tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati, Margret Taye Odofin, kudi har N42.5m da wata jami’ar banki ta kwashe mata.

Odofin ta shigar da korafi ga EFCC a watan Disamba 2024 bayan ta gano cewa jami’ar bankinta, Kehinde Yusuf, ta karkatar da kudin ajiyarta zuwa wasu asusu ba tare da izini ba.

Binciken EFCC ya gano cewa Kehinde ta tsere zuwa Burtaniya bayan badakalar ta tonu, sai dai hukumar ta bi sahunta har ta sami nasarar kwato wasu daga cikin kudin da aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com