Lamari Ya Girma: ’Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Dan Majalisa a Masallaci
- Ana zargin masu garkuwa da mutane sun sace tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Ogun yayin wani farmaki
- Rahotanni sun tabbatar da sace Hon. Maruf Musa, a ƙaramar hukumar Ogun Waterside lamarin da ya tayar da hankula
- Maharan sun harba bindiga ba kakkautawa, lamarin da ya jikkata wasu mazauna yankin kafin su tsere da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ogun Waterside, Ogun - Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace tsohon ɗan Majalisa a Ogun.
Maharan sun sace Hon. Maruf Musa, a yankin Ibiade da ke ƙaramar hukumar Ogun Waterside ta jihar.

Source: Twitter
Rahoton Tribune ya ce Maruf Musa ya kasance mamba a Majalisa ta shida ta Jihar Ogun kafin ya bar muƙamin.
Yadda yan bindiga suka addabi jihar Ogun
Jihar Ogun na daga cikin jihohi da ke fama da matsalolin tsaro wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma ba dare ba rana.
Ko a kwanakin baya ma, mun ba ku labarin yadda wasu yan bindiga suka kai mummunan hari a jihar har suka kashe babban Fasto yayin harin.
Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Ipokia ta jihar Ogun bayan ƴan bindiga sun kai hari a coci.
Ƴan bindigan ɗauke da bindigog ƙirar AK-47 sun kutsa kai cikin wurin ibadar inda suka hallaka limamin cocin mai suna Yoni Adetula.
Majiyoyi sun bayyana cewa marigayin wanda kwamandan wata rundunar tsaro ne ya daɗe yana takun saƙa da masu fasa ƙwauri.

Source: Original
Yadda aka sace tsohon dan majalisar Ogun
Majiyoyi sun ce an sace tsohon ɗan majalisar ne yayin da yake tsaka da ibadar sallar mangariba da misalin ƙarfe 7:00 na yamma, a wani masallaci da ke cikin harabar gidansa.
Sun bayyana cewa mazauna yankin sun yi ƙoƙarin ceto shi daga hannun maharan, amma duk ƙoƙarin ya ci tura yayin da aka tilasta musu ja da baya.
A cewar majiyar, waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutanen sun harba bindiga ba kakkautawa, domin tsoratar da jama’a tare da hana su kai musu farmaki.
Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu daga cikin mazauna yankin sun samu raunuka, sakamakon harbin bindigar da maharan suka yi yayin da suke tserewa.
Har yanzu ba a samu wata sanarwa a hukumance ba daga jami’an tsaro ko gwamnati dangane da lamarin.
Ana sa ran ƙarin bayani zai fito daga baya, yayin da jama’a ke jiran matakin da hukumomin tsaro za su ɗauka domin ceto tsohon ɗan majalisar tare da kamo waɗanda suka aikata wannan ta’asa.
Yan bindiga sun cakawa Fastoci wuka
Mun ba ku labarin cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kan malaman addini guda biyu mabiya darikar Katolika a Mararaba da ke jihar Nasarawa.
Lamarin ya faru ne a kusa da babban birnin tarayya Abuja, inda suka daba musu wuka da dare abin da ya tayar da hankulan al'umma.
Limaman addinin Kiristan sun samu munanan raunuka, amma an kai su asibiti cikin gaggawa kuma an ce yanayin lafiyarsu ya daidaita.
Asali: Legit.ng

