Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci kan AbdulMalik, Wanda Ya Kashe Hanifa a Kano
- Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kisa ga AbdulMalik Tanko, wanda ya kashe Hanifa Abubakar a jihar Kano
- Wannan hukunci ya biyo bayan daukaka karar da AbdulMalik ya yi bayan babbar kotun Kano ta umarci a rataye shi har lahira
- Mai shari’a A.R. Muhammad ya roki gwamnati ta gaggauta zartar da hukunci kan AbdulMalik bayan ya gama amfani da damar da doka ta ba shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan malamin makaranta, AbdulMalik Tanko, wanda ya kashe yarinya yar shekara biyar, Hanifa Abubakar a jihar Kano.
Idan baku manta ba babbar kotun Kano ta yanke wa AbdulMalik hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama shi da laifin kisan Hanifa, wacce ya yi garkuwa da ita a farko.

Kara karanta wannan
Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

Source: Facebook
Kotun daukaka kara ta yi hukunci
Leadership ta tattaro cewa bayan daukaka kara, kotun mai zama a Kano ta tabbatar da wannan hukunci na rataye AbdulMalik har lahira bisa laifin kisan Hanifa.
Mai shari’a A.R. Muhammad, wanda ya karanta hukuncin a ranar Talata, ya yi watsi da daukaka karar da AbdulMalik Tanko ya yi, tare da tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Jihar Kano.
Alkalin ya kara da cewa kotun farko ta bi doka yadda ya kamata kuma ta tantance hujjoji yadda ya dace, don haka babu dalilin da za a soke hukuncin da ta yanke.
A cewar alkalin, kotu ta gano cewa hujjojin da mai daukaka kara ya gabatar ba su da karfi, yayin da bangaren gwamnati ya gabatar da gamsassun hujjoji.
Saboda haka, Mai shari’a Muhammad ya ce babu wani dalili da zai sa kotun daukaka kara ta tsoma baki ko ta sauya hukuncin karamar kotun.
Kotu ta umarci a rataye AbdulMalik Tanko
Ya kuma bukaci gwamnati ta hanzarta zartar da hukuncin, da zarar mai laifin ya kammala bin duk hanyoyin daukaka kara da doka ta tanada.
Tun farko dai Abdulmalik Tanko, wanda shi ne shugaban makarantar da yarinyar ke karatu, ya yi garkuwa da Hanifa a watan Disamba, 2021, inda ya nemi fansar N6m daga iyayenta.
Daga bisani ya sa mata gubar bera, abin da ya yi sanadin rasuwarta, lamarin ya jawo suka da Allah wadai a fadin kasar nan, musamman ganin karancin shekarun yarinyar da kuma cin amanar da aka yi.

Source: Facebook
Yadda aka gurfanar da makashin Hanifa
An gurfanar da AbdulMalik Tanko a gaban kotu a ranar 24 ga Janairu, 2022, tare da Isyaku Hashim da Fatima Jibril, bisa tuhume-tuhumen hada baki wajen aikata laifi, garkuwa da mutum, tsare mutum ba bisa ka’ida ba, da kuma kisan kai.
A ranar 28 ga Yuli, 2022, Babbar Kotun Kano karkashin Mai shari’a Usman Na’abba ta yanke wa Abdulmalik da Isyaku Hashim hukuncin kisa ta rataya, yayin da Fatima Jibril aka yanke mata hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.
A yanzu kuma kotun daukaka kara ta tabbatar da wannan hukunci, tare da kira ga gwamnati ta hanzarta rataye wanda ya aikata kisan, kamar yadda Premium Radio ta rahoto.
An tunawa gwamnatin Kano batun kisan Hanifa
A wani rahoton, kun ji cewa Ibrahim A Khalil ya tunatar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf da cewa bai dace a manta da batun kisan Hanifa Abubakar ba.
A shekarar 2022 ne wani malamin makaranta, AbdulMalik Tanko a amsa cewa ya sace tare da kashe dalibarsa mai shekaru biyar da haihuwa.
Ibrahim ya jero wasu tambayoyi da ke neman sanin dalilin da ya sa aka jinkirta zartar da hukuncin kisa da kotu ta zartar a kan AbdulMalik Tanko.
Asali: Legit.ng

