Tashin Hankali: Ana Zargin Uwargida Ta Hallaka Mijinta saboda Ya Yi Mata Kishiya

Tashin Hankali: Ana Zargin Uwargida Ta Hallaka Mijinta saboda Ya Yi Mata Kishiya

  • Ana zargin wata uwargida ta kashe mijinta Abdul-Kadir Nagazi bayan ya auri wata matar da ta haihu kwanan nan a jihar Kogi
  • Ma'aikatan lafiya suna zargin an yi amfani da guba mai hadari wajen kashe mutumin bayan matar ta ajiye masu gawarsa a asibiti
  • Rundunar 'yan sandan Kogi ta fara farautar matar da ake zargi yayin da dangin mamacin suka fadi irin gatan da aka yi mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - Ana zargin wata mata mai suna Favour Odoba ta kashe mijinta, Momo Jimoh Jamiu, wanda aka fi sani da Abdul-Kadir Nagazi, a garin Okene da ke Jihar Kogi, saboda ya yi mata kishiya.

Majiyoyi sun bayyana cewa ma’auratan sun shafe kusan shekara tara da aure amma Allah bai nufa sun samu karuwa ta ɗa ba.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello zai nemi kwace kujerar Sanata Natasha a zaben 2027

Wata mata ta kashe mijinta saboda ya auro wata matar da ta haifa masa magaji.
Taswirar jihar Kogi, inda wata mata ta kashe mijinta saboda zafin kishi. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Uwargida ta kashe mijinta saboda ya karo aure

Rahoton Jaridar Daily Trust ya nuna cewa rikicin ya fara ne bayan mijin ya auri wata mata ta biyu wadda ta haifo masa magaji kimanin watanni biyu da suka wuce.

Wani ɗan uwan marigayin, wanda aka bayyana sunansa da Onono kawai, ya ce:

“An daura aurensa da Favour tun shekara tara da suka gabata, kuma ba ta taba haihuwa ba. Bayan ya auri wata mata, wacce har ta haifi santalelen yaro kwanan nan, sai Favour ta gayyace shi kwana a gidanta.
"Mun samu bayani cewa washe gari, an ga ta dauki gawarsa ta kai asibiti, ta kuma gudu daga nan, ba a san inda take ba.”

Wasu majiyoyin lafiya sun ce bayan an gudanar da gwaje-gwaje, an fara zargin guba ya ci a abinci, sai dai har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar a hukumance ba.

Kara karanta wannan

Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya

'Yan sanda sun fara neman uwargida

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, CSP William Aya, ya ce:

“Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya kashe shi da kuma yadda lamarin ya wakana. Wacce ake zargin ta yi kisan, matar marigayin kenan, yanzu haka ta tsere ana nemanta."

A wani bangare kuma, ɗan uwa ga marigayin, Injiniya. Abdulrazak Abdulrazeez, ya yi jawabi kan matar ɗan uwansa, Favour Odoba, wadda ake zargi da kashe shi.

Abdulrazeez, ya bayyana cewa Abdul-Kadir ya kashe sama da Naira miliyan biyu wajen buɗe babban shago domin Favour ta yi sana'a, kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.

Rundunar 'yan sanda ta ce ta fara farautar matar da ta kashe mijinta saboda ya karo mata kishiya a Kogi.
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Dan uwan mamacin ya gargadi matasa

Yayin da yake wallafa bidiyo daga jana’izar Abdulkadir a ranar Litinin, Abdulrazeez ya siffanta wadda ake zargi da “hatsabibiya a siffar mutum”, yana mai cewa ba za ta iya tserewa hukuma ba, dole wata rana a kamata.

Kara karanta wannan

Bayan farmakin Amurka a Sokoto, mayakan ISWAP sun kai kazamin hari Yobe

Ya kuma yi gargaɗi ga maza kan batun aure, inda ya ce:

“A matsayinka na saurayi, duk abin da za ka yi a rayuwa, kada ka taɓa auren yarinya ‘yar Ebira wadda ta fara hulɗar soyayya ko ta san namiji da kuruciya."

A halin yanzu, binciken ‘yan sanda na ci gaba, yayin da iyalan marigayin ke neman adalci kan mutuwarsa.

Mata ta sokawa mijinta wuka har lahira

A wani labari, mun ruwaito cewa, wata matar aure ta daba wa mijinta wuka har lahira a unguwar Abbari da ke Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Matar mai suna Zainab Isa yar kimanin shekara 22 ta hallaka mijinta Ibrahim Yahaya ɗan shekara 25 da wuƙa a lokacin da sa'insa ta barke tsakaninsu.

Da take amsa laifintaa, Zainab ta ce babu wani farin ciki a zaman aurensu, kullum cikin faɗa da tashin hankali suke musamman idan ta nemi abinci ko kuɗi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com