'Dan Kaduna Ya Zama Gwarzon Kasa, Ya Ci Kyautar Dalleliyar Mota a Wurin Musabaka a Abuja
- Aliyu Abdurrahman daga Jihar Kaduna, shi ne ya zama gwarzon shekara a gasar karatun Alkur'ani ta kasa da aka gudanar a Abuja
- Sarkin Bwari, Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro, wanda ya wakilci Mai Alfarma Sarkin Muaulmi ne ya bayyana wanda ya lashe Musabaka ta bana
- Kungiyar JIBWIS mai hedkwata a Jos, watau Izalar Jos ce ta shirya wannan musabaka, kuma ta samu tallafin makudan kudade
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Sarkin Bwari, Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro, ya ayyana gwarzon da ya lashe gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa baki ɗaya da aka gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.
Sarkin, ya wakilci Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, a wajen taron da Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) mai hedkwata a Jos ta shirya.

Source: Facebook
Dan Kaduna ya zama gwarzon shekara
Daily Trust ta ce wanda ya zama zakara gaba ɗaya shi ne Aliyu Abdurrahman daga Jihar Kaduna, wanda ya lashe matsayi na farko a rukunin hadda da tafsirin Hizb 60 na Alƙur’ani.
Musabakar, wacce aka gudanar a birnin tarayya Abuja ta samu mahalarta hafizai a rukunai daban-daban daga jihohi 25 na ƙasar nan.
Sakamakon nasarar da ya samu na zama zakaran kasa na 2025, an ba Abdurrahman kyautar dalleliyar mota, kuɗi da sauran kyaututtuka.
Sakataren Kwamitin Musabaka na Ƙasa na kungiyar JIBWIS, Alhafiz Abdulmumin Aliyu, ya sanar da sauran waɗanda suka yi nasara a rukunai daban-daban.
An raba motoci a gasar Alkur'ani ta kasa
Daga cikinsu akwai Abdullahi Salisu Yahaya da Idris Saminu Ash’hab, duk daga Jihar Kano; Ibrahim Abdullahi Nur daga Jihar Yobe; da Mahmood Muhammad daga Jihar Sokoto.
Kowane daga cikin wadanda suka samu nasara a Musabakar ta bana, an ba shi kyautar mota da kudade, kamar yadda Aminiya ta kawo.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Majalisar Malamai ta JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya nuna godiya ga duk wadanda suka bada gudummuwa wajen shirya gasar.
Kungiyar Izala ta samu tallafin kudi
Daga cikin manyan masu ba da gudummawa akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya bayar da motoci biyu, da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, wanda ya bayar da Naira miliyan 40.
’Yan Majalisar Wakilai biyu, Hon. Abubakar Kabir Bichi (Kano) da Hon. Muktar Aliyu Betara (Borno), kowane daga cikinsu ya bayar da Naira miliyan 50.

Source: Facebook
Haka kuma, Shugaban Kwamitin Kuɗi da Ayyuaka Hon. Ahmad Idris Wase, ya sanar da ƙarin alƙawuran tallafi.
Shi kansa Hon. Wase ya bayar da Naira miliyan 10, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 10 da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya bayar.
Borno da Kano sun zama zakaru a Musabaka
A wani labarin, kun ji cewa an kammala Musabaka karo na 40, wacce aka gudanar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Shugaban Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci a Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto, Farfesa Abubakar Yelwa, shi ne ya sanar da sakamakon gasar gaba daya
Ya ayyana Musa Ahmed Musa daga Borno a matsayin zakaran rukunin maza, yayin da Hafsat Muhammad Sada daga Jihar Kano ta lashe kambun a bangaren mata.
Asali: Legit.ng

