Gwamnonin Arewa 5 da Suka Kafa Jami’an Tsaron Jiha domin Kakkabe Yan Ta’adda
Jihohin Arewacin Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa duk da kokarin gwamnatocinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lamarin rashin tsaro da ya karade Arewa maso Yamma da Gabas da kuma ta Tsakiya ya hada da garkuwa da mutane da kashe-kashe da satar shanu.

Source: Facebook
Gwamnonin da suka kaddamar da jami'an tsaro
Rahoton Punch ya ce gwamnoni da dama sun kaddamar da jami'an tsaron al'umma ko jiha wadanda za su kawo karshen ta'addanci.
Mafi yawan gwamnonin da suka dauki wannan mataki sun fito ne daga Arewacin kasar musamman bangaren Yammaci da Tsakiyar Najeriya.
Wasu na ganin jami'an tsaron sun taimaka wurin rage tashin hankali yayin da wasu ke ganin su kansu jami'an tsaron na cin zarafin al'umma.
Legit Hausa ta duba jihohin Arewa da suka kaddamar da jami'an tsaro musamman domin ganin bayan ta'addanci.
1. Gwamna Caleb Muftwang - Plateau
Gwamna na baya bayan nan da ya kaddamar da jami'an tsaro a jiharsa domin yaki da ta'addanci shi ne Caleb Mutfwang na Plateau.
Gwamnatin Jihar a ranar Talata 23 ga watan Disambar 2025 ta kaddamar da sababbin jami’ai 1,450 da aka horar.
An kaddamar da jami'an tsaron na rundunar 'Operation Rainbow' ne a wani mataki na kara karfafa tsaro a fadin jihar.
Gwamna Caleb Mutfwang, wanda ya jagoranci taron, ya ce jihar ta ba tsaro muhimmanci a matsayin ginshikin zaman lafiya da ci gaba, cewar Premium Times.
Da yake jawabi ga sababbin jami’an, Mutfwang ya ce aikinsu shi ne kare rayuka da dukiyoyi, yana mai gargadinsu da su yi aiki cikin bin doka da oda.
A cewarsa, rundunar 'Operation Rainbow' tana aiki ne a matsayin bangare na tsarin tsaron jihar, tare da hadin gwiwa da sojoji, ‘yan sanda da Hukumar NSCDC.

Source: Facebook
2. Gwamna Abba Kabir Yusuf - Kano

Kara karanta wannan
Bayan Sakkwato, an jero jihohi 7 da ya kamata Amurka ta kawo hari a Arewacin Najeriya
Yayin da Kano ta fara fuskantar matsalolin tsaro da suka shafi ta'addanci da satar mutane a wasu yankuna, gwamnatin jihar ta fara daukar matakai.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da hukumar tsaro ta jiha mai suna 'Kano State Neighbourhood Watch Corps' a filin wasa na Sani Abacha.
Gwamnati ta kaddamar da hukumar ne a yayin da Kano ta fara fama da barazanar tsaro a wuraren da ke iya da Katsina.
Mai Magana da yawun gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa za a tura jami’ai 2,000 zuwa kananan hukumomi 44 domin yaki da manyan laifuffuka.

Source: Facebook
3. Gwamna Dauda Lawal Dare - Zamfara
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalolin ta'addanci a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Gwamna Dauda Lawal na jihar ya ɗauki ɗamarar yaƙar ƴan bindigan da suka addabi jihar domin kawo karshen masifar.
Gwamnan ya ƙaddamar da sabuwar rundunar 'Community Protection Guards' wacce za ta yi fito na fito da ƴan bindiga a jihar.
Rundunar wacce aka fi sani da Askarawan Zamfara ta ƙunshi jami'ai 2,645 waɗanda aka zaɓo su daga ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Source: Facebook
4. Gwamna Ahmed Aliyu - Sokoto
Jihar da ta kasance cikin wadanda suka kaddamar da jami'an tsaro ita ce Sokoto a kokarin kawo karshen matsalar da kare rayukan al'umma.
Gwamnatin jihar Sokoto ta kaddamar da sabuwar rundunar tsaron al'umma, domin taimakawa sauran jami'an tsaro.
Da ya ke rattaba hannu kan dokar kafa rundunar tsaron, Gwamna Ahmed Aliyu ya ce rundunar tsaron ba kishiyar 'yan sanda ba ce.
Gwamnan jihar ya kuma ce wannan matakin zai taimakawa gwamnatin Shugaba Tinubu ya tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al'umma.

Source: Facebook
5. Gwamna Dikko Umaru Radda - Katsina
Malam Dikko Umaru Raɗda ya kaddamar da sabuwar rundunar tsaron al'umma domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Katsina.
Gwamnan ya ce dakarun rundunar za su ƙara ƙarfafa jami'an tsaro wajen shiga daji da yaƙi da yan bindiga a jihar.
Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da Abba Gida-Gida na cikin waɗanda suka halarci taron.

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara bayan gwabza fada da 'yan bindiga a jihar Kano

Source: Instagram
Amurka ta kai hari a jihar Sokoto
A baya, mun ba ku labarin cewa kasar Amurka ta ce ta kai hare-hare kan yan ta'adda da ke Arewa maso Yammacin Najeriya bisa bukatar gwamnati.
Harin ya auku a Arewa maso Yammacin kasar, a yankin jihar Sokoto da kuma yankin Offa a Kwara inda jama'a suka ji ƙarar da ta girgiza wasu gidaje.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kai harin ne bayan gargaɗin cewa hakan za ta faru idan ba a daina kashe Kiristoci ba.
Asali: Legit.ng

