Manyan Abubuwa 6 da za Su Faru a Najeriya a Sabuwar Shekarar 2026
Yayin da shekarar 2025 ke shirin bankwana, Legit Hausa ta yi dubu kan masu muhimman abubuwa da ake sa ran za su faru a Najeriya a 2026.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Al'ummar Najeriya na shirye-shiryen fuskantar rayuwa a 2026 yayin da 2025 za ta yi bankwana a 'yan kwanaki masu zuwa.
Gwamnatin tarayya, 'yan siyasa, kamfanoni da 'yan kasuwa a Najeriya sun gabatar da abubuwan da suke son gudanarwa a shekara mai zuwa.

Source: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa ta kawo muku wasu daga cikin muhimman abubuwan da ake sa ran za su faru a kasar nan da za za su shafi jama'a.
1. Dokokin Haraji za su fara aiki a 2026
Bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokokin haraji da majalisar kasa ta amince da su, an bayyana cewa za su fara aiki a Janairun 2026.
A kwanakin baya, wani dan majalisar wakilai, Hon. Abdussamad Dasuki daga jihar Sokoto ya bayyana cewa dokokin da fadar shugaban kasa ta wallafa sun saba da wadanda majalisa ta amince da su.

Source: Twitter
Hakan ya sanya kira daga shugabanni da 'yan siyasa, ciki har da Atiku Abubakar a kan a dakatar da aiwatar da dokokin a Janairun 2026 har sai an yi bincike.
Sai dai duk da haka, Daily Trust ta rahoto fadar shugaban kasa ta ce babu gudu ba ja da baya game da aiwatar da dokar a farkon 2026.
2. Dangote zai fara raba mai kyauta a 2026
A bangaren makamashi, matatar Dangote ta bayyana cewa za ta fara raba man fetur kyauta ga abokon huldarta daga watan Janairu, 2026.
Leadership ta wallafa cewa lamarin zai shafi ƙungiyoyin ’yan kasuwa, musamman bayan kungiyar IPMAN ta yi kira ga dukkan mambobinta a faɗin ƙasar nan da su riƙa sayen man fetur daga matatar Dangote.

Source: Facebook
Ana fatan cewa wannan tsari zai taimaka wajen rage farashin man fetur a ƙasar nan domin rage wa jama'a wahalar rayuwa da suke fama da ita.

Kara karanta wannan
Manyan matakai 8 da gwamnatin Tinubu ta dauka kuma suka ja hankalin 'yan Najeriya a 2025
3. Dokar cire kudi za ta fara aiki a 2026
Bankin CBN ya soke kayyade adadin kuɗin da ake iya ajiyewa a bankuna, tare da sabunta wasu dokoki da suka shafi mu'amalar kuɗi da za su fara aiki a farkon 2026.
Sabon tsarin ya kara adadin kudin da za a iya cirewa a mako daga N100,000 zuwa N500,000 ga mutum ɗaya da Naira miliyan 5 ga kamfanoni.

Source: Getty Images
CBN ya wallafa cewa ya soke tsarin da ya bai wa mutum damar cire N5m sau daya a wata da kuma Naira miliyan 10 ga kamfanoni, wanda a baya ake bukatar samun izini na musamman.
4. Zaben gwamna a Ekiti da Osun a 2026
Hukumar zaɓe ta kasa INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Ekiti da Osun a ranakun 20, Yuni, 2026 da 8, Agusta, 2026.
INEC ta ce waɗannan ranaku sun yi daidai da tanadin doka na fitar da sanarwar manyan zaɓe aƙalla kwanaki 360 kafin ranar da za a gudanar da su.

Source: Facebook
Rahoton Business Day ya nuna cewa INEC ta bayyana cewa hukumar ta amince da cikakken jadawalin lokaci da tsarin ayyuka na zaɓukan jihohin biyu.
5. Za a yi babban taron APC a 2026
Jam’iyyar APC ta fitar da cikakken jadawalin tarukan wakilai daga matakin unguwa zuwa na ƙasa na 2025/2026, wanda zai kai ga babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka tsara gudanarwa a watan Maris, 2026.
Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ne ya sanar da hakan kamar yadda Vanguard ta rahoto, inda ya ce an tsara jadawalin ne bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar, domin zaɓen shugabanni a dukkan matakai.
Rahotanni sun nuna cewa jam'iyyar za ta gudanar da tarukan jihohi a ranar 7, Maris, 2026, bayan kammala tantance ’yan takara da sauraron ƙorafe-ƙorafe.

Source: Twitter
Daga ƙarshe, jadawalin ya nuna cewa babban taron jam’iyyar APC na ƙasa zai gudana daga ranar 25 zuwa 28, Maris, 2026, inda ake sa ran za a kammala zaɓen shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa.
6. Gangar zaben 2027
Bisa al'ada, kafin shekara mai zuwa ta zo karshe za a ji hukumar INEC ta janye takunkumin kamfe, ta ba 'yan siyasa damar fara yakin neman kuri'a.
Babu mamaki nan da 'yan watanni INEC ta fitar da jadawalin zabe wanda zai bude kofar fara saida fam, zaben tsaida gwani da kuma yawon yin kamfe.
Akwai yunkurin sauya lokacin zabe, ko da ba a yi nasarar hakan ba, a badi za a fara kamfe gadan-gadan domin tunkarar babban zabe a farkon watannin 2027.
Abba Kabir Yusuf zai koma APC
A wani labarin, mun kawo muku cewa an fara rade radi game da makomar siyasar Kano yayin da aka ce Abba Kabir Yusuf zai koma APC.
Hadimin tsohon shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa wata majiya mai tushe ta tabbatar masa da cewa gwamnan zai sauya sheka.
Wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnan zai sauya sheka ne kafin taron APC na 2026 domin samun damar karbar ragamar jam'iyyar a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


