Tashin Hankali: Bam Ya Tashi da Mutane a Masallaci ana Sallar Magriba a Maiduguri
- Ana zargin wani 'dan kunar bakin wake ya tashi bam ana cikin sallar Magriba a Masallacin Juma’a na Gambarou da ke Maiduguri
- Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun rasa rayukansu, wasu kuma sun samu raunuka daban-daban a harin
- Duk da babu sanarwa daga rundunar 'yan sanda a hukumance amma wadanda suka tsira sun shaida abin da ya faru a masallacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Maidiguri, Nigeria - Wani abin fashewa (IED) da ake kyautata zaton bam ne ya tashi da mutane a masallaci ana cikin sallar Magariba a jihar Borno.
Rahotonni sun nuna cewa wani dan kunar bakin wake ne ya tashi bam din da misalin karfe 6:00 na yammaci a wani masallacin Gamboru a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Source: Original
An kai harin bam masallaci a Maiduguri
Majiyoyi sun tabbatar wa jaridar Vanguard cewa masallacin na tara mutane da dama a kullum, ciki har da ’yan kasuwa da masu sayar da kaya da ke harkokinsu a Kasuwar Gamboru.
An tattaro cewa mutanen Maiduguri da ke Arewa maso Gabas sun dauki tsawon lokacin rabon ba su fuskanci harin bam, wanda ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP da daukar nauyi.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na ’Yan Sanda (PPRO), ASP Keneth Daso, ba, domin layukan wayarsa ba su shiga ba.
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ya tabbatar da fashewar bam din a Masallacin Juma’a na Gambarou a Maiduguri a shafinsa na X
Ya ce wani dan kunan bakin wake ne ya tayar da bam din bayan ya shiga masallacin a boye, kuma mutane da dama sun mutu.
Mutane da dama sun mutu a harin masallaci
Wasu daga cikin masu ibadar da suka tsira daga harin sun ce maharin ya shige cikin masallacin ne a ɓoye, sannan ya tayar da bam a lokacin da ake tsaka da sallar Magariba ta jam’i.
Wani daga cikin shaidun gani da ido ya ce:
"Dan kunar bakin waken ya tayar da bam din ne a lokacin raka’a ta farko ta sallar Magariba. Mutane da dama sun mutu, yayin da wasu suka samu raunuka daban-daban.”

Source: Facebook
Sai dai zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin. Duk da haka, ana zargin ƙungiyar Boko Haram, wadda ta sha kai hare-haren kunar bakin wake da dama a yankin cikin ’yan watannin da suka gabata.
An tashi bam a kusa da sojoji a Borno
A wani rahoton, kun ji cewa 'dan kunar bakin wake ya kashe sojoji biyar a yankin Pulka, da ke cikin karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Ana zargin dan kunar bakin waken na daga cikin ‘yan kungiyar Boko Haram , kuma ya fito ne daga maboyarsu da ke tsaunukan Mandara, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.
Majiyoyi sun ce dan ta’addan ya fake da zama matafiyi, inda ya karaso kusa da sojojin da ke bakin aiki kafin ya tayar da bam din da ke jikinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

