Daga Masallatai zuwa Gidaje: EFCC Ta Bankado Kadarori 41 na Abubakar Malami da Iyalansa

Daga Masallatai zuwa Gidaje: EFCC Ta Bankado Kadarori 41 na Abubakar Malami da Iyalansa

Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce ta gano kadarori guda 41 da suke da alaka da Abubakar Malami, tsohon babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kadarorin sun haɗa da otal-otal, gidajen zama na alfarma, filaye, makarantu da kamfanin ɗab'i, kuma suna a jihohin Kebbi, Kano da birnin Abuja.

EFCC ta bankado wasu kadarori da suke da alaka da tsohon minista, Abubakar Malami.
Abubakar Malami, tsohon ministan shari'a da EFCC ta bankado wasu kadarori 41 da ke da alaka da shi. Hoto: @aamalamiSAN, @officialEFCC
Source: Twitter

Rahoton The Cable ya nuna cewa kadarorin da ke Kebbi sun kai darajar N162,195,950,000, na Kano sun kai N16,011,800,000, yayin da kadarorin da ke Abuja suka kai darajar N34,685,000,000.

Gwamnatin tarayya ta kuma shigar da tuhume-tuhume 16 na safarar kuɗi a kan Malami da ɗansa, Abdulaziz Malami, bisa sashe na 15, 18 da 21 na dokar hana safarar kuɗi, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta ba da belin Malami, ta sanya sharudda masu tsauri ga tsohon minista

Jaridar ta rahoto cewa ta samu cikakken jerin kadarorin da ake dangantawa da Malami, kamar haka:

Kadarorin Jihar Kebbi

Jimillar kima: N162,195,950,000

Jami'a da makarantun Rayhaan

  • Matsugunnin jami'ar Rayhaan na dindindin: N56bn
  • Matsugunnin jami'ar Rayhaan na wucin gadi: N37.8bn
  • Matsugunnin jami'ar Rayhaan na uku: N2.45bn
  • Gidan shugaban jami'a (V.C): N490m
  • Rayhaan Model Academy: N11.2bn
  • Makarantar firamare da sakandaren Rayhaan: N8.75bn

Masana’antu da Kasuwanci

  • Gine-ginen masana’anta: N4.2bn
  • Injuna da na’urori: N10.5bn
  • Masallacin masana’anta: N2.45bn
  • Gidajen ma’aikata (10): N1.487bn
  • Ginin Rayhaan Bustan: N3.15bn
  • Kamfanin ɗab'i: N1.05bn
  • Garejin tankoki na Al-Afiya Energy: N2.45bn
  • Kamfanin Amasdul Oil and Gas: N1.05bn
  • Gidan rediyon Rayhaan: N78.75m

Azbir Brand

  • Otal din Azbir: N10.325bn
  • Wurin tallar kayayyaki: N581m
  • Wurin shakatawa: N392m
  • Masallaci: N252m
  • Kamfanin dinka suturu na Azbir: N350m
  • Kantin sayar da magunguna da na kayan masarufi na Azbir: N175m

Gidaje da gine-gine

  • Gidan Malami GRA: N350m
  • Gida bayan Mobil: N490m
  • Gida bayan makabarta: N350m
  • Gidan Abdulaziz (ɗan fari): N1.659bn
  • Gidan Ahbiru (ɗa na biyu): N2.989bn
  • Ginin kungiyar ba da tallafi ta Malami: N210m
  • Gidauniyar Kadi Malami: N56m
  • Gidan masu gadi na Rayhaan: N245.7m
  • Gini mai hawa uku da ba a kammala ba: N665m

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta shigar da korafe korafe 16 kotu kan Abubakar Malami da ɗansa

Kadarorin jihar Kano

Jimillar kima: N16,011,800,000

  • Otal din Zeennoor: N11.2bn
  • Masallacin Zeennoor: N84m
  • Tsohon ginin otal din Zeennoor: N280m
  • Otal din Rayhaan Kano: N2.24bn
  • Wurin motsa jiki na Rayhaan Kano: N1.225bn
  • Gidan matar Malami (Ahmadu Bello Way): N982.8m

Kadarorin Abuja

EFCC ta ce kadarorin da aka gano suna a Kano, Kebbi da Abuja.
Abubakar Malami, tsohon ministan shari'a yana magana da manema labarai. Hoto: @AZarummai
Source: Twitter

Jimillar kima: N34,685,000,000

  • Gidan alfarma a Maitama: N5.95bn
  • Otal din Meethaq a Jabi: N8.4bn
  • Otal din Meethaq a Maitama: N12.95bn
  • Gidan alfarma a Efab Estate: N385m
  • Otal din Harmonia a Area 11 Garki: N7bn

Jimillar darajar dukiyar gaba ɗaya: N212,892,750,000.

Kotu ta ba da belin Abubakar Malami

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, wata babbar kotu da ke Abuja ta ba da belin tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN) a takaddamarsa da EFCC.

Mai shari'a Bello Kawu ne ya amince da buƙatar belin a ranar Talata, 23 ga Disamba, 2025 biyo bayan wani koke da lauyoyin Malami suka shigar gabansa.

An bayar da belin Malami ne a kan sharuɗɗan da suka haɗa da miƙa fasfo ɗin tsohon ministan na fita ƙasashen waje da kuma samar da mutane biyu da za su tsaya masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com