Haƙar Ma'adinai: 'Yan China Sun Ɗauki Zafi kan Zargin Hura Wutar Ta'addanci a Najeriya
- Kungiyar 'yan kasar China masu hakar ma'adinai ta yi magana kan zargin kara wutar ta'addanci a Najeriya
- 'Yan kungiyar sun musanta zargin cewa kamfanonin hakar ma’adinan China na taimaka wa ta’addanci a kasar
- Zargin ya biyo bayan wani rahoto da ya tuhumi Sinawa da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, gurbata muhalli da sauransu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar masu hakar ma'adinai daga China ta yi karin haske kan zargin tallafawa ta'addanci a Najeriya.
Kungiyar ta yi watsi da zargin cewa kamfanonin China da ke hakar ma’adinai a Najeriya suna aikata laifuffuka ko taimaka wa ta’addanci.

Source: Facebook
Zargin kamfanonin China da alaka da ta'addanci
Wannan martani ya biyo bayan rahoton 'Renevlyn Development Initiative' na 11 ga Disamba, 2025 na zarginsu da ta'addanci, cewar Punch.
Rahoton ya zargi wasu ‘yan China da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, gurbata muhalli, lalata tattalin arziki, da kuma alakanta su da tallafa wa ta’addanci.
Ya auna shekarun 2018 zuwa 2025, yana mai da hankali kan abubuwan da suka faru tun 2022, tare da kiran gwamnati ta inganta tsarin kula da bangaren.
Martanin 'yan China kan zargin ta'addanci
A wata sanarwa da aka fitar, kungiyar ta ce zarge-zargen karya ne, marasa tushe, kuma suna yaudarar jama’a gaba ɗaya.
Kungiyar ta ce kamfanonin hakar ma’adinan China suna bin dokokin Najeriya yadda ya kamata, karkashin jagorancin gwamnatin kasar China.
Ta kara da cewa kamfanonin suna aiki tare da hukumomin Najeriya domin inganta bangaren, tare da saka jari a masana’antun sarrafa ma’adinai na cikin gida.

Source: Facebook
Yadda ake samun ayyuka ta hakar ma'adinai
Kungiyar ta bayyana cewa kamfanoninta sun dauki dubban ‘yan Najeriya aiki, lamarin da ke kara samar da ayyukan yi da darajar ma’adinai a cikin kasa.
Ta ce kamfanonin sun tallafa wa al’ummomin da suke aiki a cikinsu tare da aiwatar da shirye-shiryen kare muhalli a yankuna daban-daban, cewar rahoton Vanguard.
Dangane da zargin alaka da ta’addanci, kungiyar ta ce hakan ba shi da tushe, tana mai cewa kamfanoninta sun sha fama da hare-haren ‘yan ta’adda.
Ta ce kamfanonin China suna shirye su hada kai da gwamnatin Najeriya wajen yaki da rashin tsaro domin samar da muhallin kasuwanci mai aminci.
Kungiyar ta yi kira ga kafafen yada labarai da jama’a su rika bayar da rahoto cikin adalci, tana gargadin yada labaran da ba a tantance ba.
Zamfara: Gwamnati ta dage haramcin hakar ma'adinai
Kun ji cewa bangaren haƙar ma'adanai a Zamfara zai farfaɗo yayin da gwamnatin tarayya ta ɗage takunkumin da aka sanya masa a 2019.
Ministan ma'adanai, Dele Alake, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ɗage haramcin haƙar ma'adanai a jihar Zamfara.
Dele Alake ya yi nuni da cewa an yi hakan ne bayan samun ƙaruwar yanayin tsaro mai kyau a jihar da ake fama d 'yan bindiga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

