Bincike ya fallasa yadda masu hakar gwal ta bayan-fage su ke hura wutan rashin tsaro

Bincike ya fallasa yadda masu hakar gwal ta bayan-fage su ke hura wutan rashin tsaro

- Hako ma’adanai da ake yi a Zamfara ya na cikin dalilan rashin zaman lafiya

- Bincike ya nuna akwai alaka tsakanin hake-haken gwal da rikicin da ake yi

- ‘Yan siyasa sun hada-kai da kamfanonin ketare su na satar gwal a garuruwa

Shakka babu akwai arzikin ma’adanai a Najeriya, a 2017 akwai sama da mutane 600, 000 da ke cin abinci da hake-haken ma’adanai a kasar nan.

Sai dai yanzu bata-gari sun shiga cikin harkar, su na hako ma’adanai ta bayan-fage. Wani bincike da ISS Africa ta gudanar, ya tabbatar da wannan.

Wasu ‘yan siyasan Najeriya sun hada-kai da kamfanonin kasar Sin, su na hako gwal a boye, hakan ya ta’azzara rikici a kauyukan yankin Zamfara.

Ana hasashen cewa 80% na gwal din da ake hako wa a Arewa maso yamma ya na zuwa ne ta baraunyiar hanya, ba tare da sanin hukumomi ba.

KU KARANTA: Me dokar hana jiragen sama tashi a Zamfara take nufi?

Wani masani a jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Dr, Chris Kwaja, ya ce masu hako ma’adanai su na hura wtar rikici saboda su ci karensu babu babbaka.

Siyasa ta shiga rikicin domin akwai wadanda gwamnati ta ke ba kariya su cigaba da wannan aiki.

A wani bangare, daga cikin masu hake-haken ba tare da an sani ba, akwai masu huro rikicin makiyaya da manoma saboda kauyukan su ki zaunuwa.

Masu hako ma’adanan su na yi wa wasu ‘yan siyasa aiki ne, su kuma su kan hada-kai da kamfanonin ketare, a wajen cinikin gwal a birnin Dubai.

Bincike ya fallasa yadda masu hakar gwal ta bayan-fage su ke hura wutan rashin tsaro
Hake-haken gwal Hoto: issafrica.org
Asali: UGC

KU KARANTA: Dalibar Jangebe ta gane daya daga cikin ‘Yan bindigan da su ka sace su

Wannan bincike ya nuna cewa ana tsere wa da gwal-gwalai ne ta iyakokin Jamhuriyar Nijar da Togo.

Duk da gwamnati ta haramta hake-haken ma’adanai a Zamfara, bincike ya nuna hor gobe ba a fasa ba.

A ranar Lahadin nan, 7 ga Watan Afrilun 2019, gwamnatin kasar nan ta bada sanarwar cewa an dakatar da duk wani aiki da ya shafe hake-hake a Zamara.

Fiye da mutane 5, 000 ne su ka mutu a jihar Zamfara kawai a dalilin wannan rikici da ya shiga Katsina, Sokoto, Kebbi, da Kaduna daga 2014 zuwa yau.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel