EFCC: Kotu Ta ba da Belin Malami, Ta Sanya Sharudda Masu Tsauri ga Tsohon Minista

EFCC: Kotu Ta ba da Belin Malami, Ta Sanya Sharudda Masu Tsauri ga Tsohon Minista

  • Kotu ta ba da belin tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami a takaddamarsa da EFCC
  • Mai shari'a Bello Kawu ya ba da belin ne saboda tsananin kunci da Malami ya ce yake fuskanta, amma ya gindaya sharudda masu nauyi
  • Rahoto ya nuna cewa ana zargin tsohon ministan da daukar nauyin ayyukan ta'addanci da kuma badakalar kudaden Janar Sani Abacha

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma ministan shari'a Abubakar Malami (SAN).

An ba da belin Abubakar Malami ne bisa tsari na wucin gadi a wata shari'a da ta shafi hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC).

Kotu ta ba da belin tsohon ministan shari'a Abubakar Malami
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami da kotu ta ba da belinsa. Hoto: @aamalamiSAN
Source: Twitter

Kotu ta kafa sharudan belin Abubalar Malami

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, jigonta kuma tsohon kwamishina yar bar duniya

Mai shari'a Bello Kawu ne ya amince da buƙatar belin a ranar Talata, biyo bayan wani koke da lauyoyin Malami suka shigar gabansa, in ji rahoton Daily Trust.

A cewar umarnin kotun, an bayar da belin Malami ne a kan sharuɗɗa irin waɗanda EFCC ta gindaya a baya, waɗanda suka haɗa da miƙa fasfo ɗin tsohon ministan na fita ƙasashen waje da kuma samar da mutane biyu da za su tsaya masa.

Lauyan Malami, Bello Doka, ya bayyana cewa waɗanda za su tsaya masa dole ne su haɗa da Darakta Janar na hukumar ba da tallafin shari'a da kuma wani ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Augie da Argungu.

Zarge-zarge da dalilan bayar da belin

Mai shari'a Kawu ya bayyana cewa ya amince da belin ne saboda dalilai na fuskantar tsananin kunci da wanda ake ƙara yake yi, har sai an saurari ƙwaƙƙwaran ƙorafe-ƙorafen da aka shigar.

Kotun ta lura cewa Malami ya riga ya cika wasu sharuɗɗan belin da aka gindaya masa tun a watan Nuwamban 2025.

Jaridar Punch ta rahoto cewa kotun ta sanya ranar 5 ga watan Janairu, 2026, a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraron ƙarar.

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi na'am a kashe masu garkuwa da mutane, gwamnati ta ki yarda

An rahoto cewa EFCC na zargin Malami da karkatar da wasu kudade.
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami da EFCC ke zarginsa da aikata rashawa. Hoto: @aamalamiSAN, @officialEFCC
Source: Twitter

Malami ya na fargaba kan shari'arsa da EFCC

Hukumar EFCC ta tsare Malami ne tun ranar 8 ga watan Disamba, 2025 bisa zarge-zargen da suka shafi tallafa wa ta'addanci, da kuma wasu al'amura da suka shafi yadda aka sarrafa kuɗaɗen Abacha da aka dawo da su Najeriya.

Ko da yake ba a fito da cikakkun bayanan zargin a fili ba, amma tsohon ministan ya yi jayayya cewa ci gaba da tsare shi ya jefa shi a mawuyacin hali, kuma hakan zai iya kawo cikas ga haƙƙinsa na samun adalci.

Magatakardar babbar kotun Abuja, Hadiza Sambo Gwandu ce ta sanya hannu a kan takardar bayar da belin wucin gadi ga tsohon minista, Abubakar Malami.

Gwamnatin Tarayya ta shigar da karar Malami

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta shigar da shigar da korafe-korafe kan tsohon ministan shari'a a Najeriya, Abubakar Malami a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Kotu ta gindaya sharudda masu tsauri kafin sakin Ministan Buhari, Ngige

An shigar da karar ne a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ake zargin Malami da aikata laifukan boye kudaden haram da suka kai Naira biliyan bakwai.

Gwamnatin tarayya, ta hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce wadannan laifuka sun sabawa dokokin mu'amala da kudi na shekarar 2011 da 2022.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com