Gwamnatin Tinubu Ta Shigar da Korafe Korafe 16 Kotu kan Abubakar Malami da Ɗansa
- Gwamnatin tarayya ta shigar da shigar da korafe-korafe kan tsohon ministan shari'a a Najeriya, Abubakar Malami
- An shigar da tuhume-tuhume 16 na safarar kudi kan Abubakar Malami SAN, bisa zargin boye kudaden haram
- 'Dansa Abdulaziz da Bashir Asabe sun gurfana a kotun tarayya Abuja, kan zargin mu’amalar biliyoyin Naira ta kamfanoni
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shigar da tuhume-tuhume 16 kan tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami bisa zargin safarar kudi.
An shigar da karar ne a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ake zargin Abubakar Malami da aikata laifuffukan boye kudaden haram.

Source: Facebook
Daga cikin wadanda ake tuhuma tare da Malami akwai dansa, Abubakar Abdulaziz Malami, da Bashir Asabe, ma’aikaciyar kamfanin Rahamaniyya, cewar TheCable.
Abubakar Malami ya magana kan tuhumarsa a EFCC

Kara karanta wannan
Zargin badakalar N4.6bn: EFCC ta shirya fara shari'a da Kwamishinan kudi a Bauchi
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tuhumar tsohon ministan a gwamnatin Muhammadu Buhari kan zargin badakala.
A kwanakin nan, ya fito ya yi magana kan dalilin da ya sa hukumar ke ci gaba da tsare da wanda ya koka kan wasu lamura.
Tsohon ministan ya ce EFCC ta ci gaba da tsare shi saboda an soke belinsa ba tare da dalili mai karfi ba.
Malami ya karyata zargin daukar nauyin ta’addanci da mallakar asusun banki 46, yana mai cewa zarge-zarge ne da ba su da tushe.
EFCC dai ta ce ta soke belin Malami ne saboda bai cika sharuddan da aka gindaya masa ba, ikirarin da lauyan ya fito ya karyata.

Source: Twitter
Abin da tuhume-tuhumen ke dauke da su
Takardar tuhume-tuhumen ta nuna cewa daga 2022 zuwa 2025, Malami da dansa sun yi amfani da wata salo domin boye kudin N1.01bn, cewar Daily Post.
Gwamnati ta kuma ce an boye kudin N600m a asusun bankin Sterling da cewa wadanda ake tuhuma sun san kudin na da alaka da laifi.
A wata tuhuma, an ce an biya N500m domin sayen katafaren gida a Maitama, Abuja, inda ake zargin kudin ya fito daga haramtacciyar hanya.
Haka zalika, an zargi Malami da wasu da hada baki wajen boye N1.04bn ta asusun otal din Meethaq tsakanin shekarar 2022 da 2024.
Gwamnati ta kara da cewa Malami da dansa sun mallaki fiye da N1.36bn ta hanyar asusun banki, duk da sanin kudin na haram ne.
Sauran tuhume-tuhumen sun hada da sayen kadarori a Garki da Jabi da kudaden da suka kai N700m da N850m.
Gwamnatin tarayya ta ce wadannan laifuka sun sabawa dokokin mu'amala da kudi na shekarar 2011 da 2022.
Hukumomi sun gano kadarori masu darajar biliyoyin Naira da ake zargin suna da alaka kai tsaye da tsohon Ministan Shari’ar Najeriya.
Zarge-zargen Malami kan shugaban EFCC
Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami SAN, ya koka kan ci gaba da tsare shi da hukumar EFCC ke yi.
Abubakar Malami ya yi zargin cewa shugaban EFCC ya kullace shi saboda wasu abubuwa da suka faru a baya.
Tsohon Ministan ya ba hukumar EFCC wa'adin lokacin da za ta sake shi ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
