Zargin Badakalar N4.6bn: EFCC Ta Shirya Fara Shari'a da Kwamishinan Kudi a Bauchi

Zargin Badakalar N4.6bn: EFCC Ta Shirya Fara Shari'a da Kwamishinan Kudi a Bauchi

  • Hukumar yaki da rasahawa ta EFCC za ta gurfanar da Yakubu Adamu, kwamishinan kudi na Jihar Bauchi a gaban kotun tarayya Abuja
  • Ana shirin gurfanar da shi a ranar Laraba 24 ga watan Disamba, 2025 tare da kamfanin Ayab Agro Products and Freight a kan zargin almundahana
  • Ana zargin ya yi laifin ne yayin da yake shugabantar reshen Polaris Bank a Bauchi, inda ya yi haɗin gwiwa da wasu mutane biyu don halatta kudin haram

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) za ta gurfanar da Yakubu Adamu, kwamishinan kudi na Jihar Bauchi a gaban kotu.

Hukumar na shirin gurfanar da shi tare da kamfanin Ayab Agro Products and Freight a gaban kotun tarayya Abuja ranar Laraba, 24 ga Disamba 2025.

Kara karanta wannan

zarge zargen rashawa: Cikakken jerin sunayen ministocin Buhari da EFCC ta cafke

EFCC ta gurfanar da jami'in gwamnatin Bauchi a gaban kotu
Ola Olukayode, Shugaban hukumar EFCC a Najeriya Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa ana tuhumarsu ne kan zargin wanke-wanken kudi har Naira biliyan 4.65 a cikin shari’ar da aka yi rajista da lamba FHC/ABJ/CR/694/2025.

EFCC na shirin shari'a da jami'in gwamnatin Bauchi

A cikin karar da aka shigar ranar 19 ga Disamba 2025 ta hannun Samuel Chime daga sashen shari’a na EFCC, Yakubu Adamu shi ne wanda aka fara tuhuma.

Daily post ta wallafa cewa shari’ar da aka sa ran za a yi a ranar Talata ta samu tsaiko saboda rashin halartar lauyoyin EFCC da kuma masu tuhumar.

Duk da haka, lauyoyin da ke kare Adamu da kamfanin, karkashin jagorancin Gordy Uche, SAN, sun halarci kotu amma Alkalin kotu, Emeka Nwite, ta dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga Disamba, 2025.

EFCC na zargin jami'in gwamnatin Bauchi da almundahana
Shugaban EFCC na kasa, Ola Olukayode Hoto: Economic anad Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Haka kuma EFCC na tuhumar kamfanin Ayab Agro Products and Freight ya kasance na biyu da ake zargi da hada baki da jami'in gwamnatin wajen almundahana.

Kara karanta wannan

Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC

EFCC ta ce Yakubu Adamu ya yi laifin ne yayin da yake reshen bankin Polaris a Bauchi, inda ya yi haɗin gwiwa da Ishaku Mohammed Aliyu da Muntaka Mohammed Duguri daga Yuni zuwa Disamba 2023.

Zargin da EFCC ke yi wa kwamishinan Bauchi

Ana zargin cewa sun tura kudi, an ɓoye su sannan an yi amfani da kudin da ba bisa doka ba, wanda bankin Polaris ya bayar a matsayin tallafin sayen babura ga gwamnatin Jihar Bauchi.

Duk da haka, baburan ba a kawo su ba, wanda hakan ya saba da sashe na 21(a) na dokar halatta kudin haram na shekarar 2022.

EFCC ta ce Yakubu Adamu da wasu sun yi amfani da wasu asusun mutane uku ko na kamfanoni don raba wani ɓangare na kudin ba bisa doka ba.

Haka kuma, hukumar ta ce Naira miliyan 165.9 an ce an tura zuwa Ayab Agro Products ta hannun kamfanin I.S. Makayye Investment Resources wanda ake ganin wani ɓangare ne na kudin.

EFCC ta cafke Akanta Janar a Bauchi

A baya, mun wallafa cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) sun cafke Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sirajo Jaja, tare da Aliyu Abubakar na kamfanin Jasfad Resources Enterprise.

Kara karanta wannan

Bangarori 4 da Tinubu zai fi kashewa kudi a kasafin 2026

Bayan Akanta Janar da aka kama, EFCC ta cika hannunta da Sunusi Ibrahim Sambo, mai sana’ar POS, kan zargin wawure Naira biliyan 70 da karkatar da kudin talakawan jihar Bauchi.

An kama Sirajo Jaja ne a Abuja ranar Laraba, 19 ga Maris, 2025, yayin da Aliyu Abubakar ya tsere bayan an ba shi belin, amma daga bisani EFCC ta sake kama shi ta ci gaba da bincike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng