‘Dalilin da Ya Sa ba a Tuhumi Jonathan kan Zargin $2.1Bn Na Kudin Makamai ba’
- Tsohon shugaban rikon kwarya na EFCC, Ibrahim Magu, ya yi magana kan zargin kwashe kudin makamai lokacin Goodluck Jonathan
- Magu ya ce ba a gayyaci Jonathan ba kan badakalar makaman $2.1bn saboda takardu sun nuna ba a amince da kudin don kamfen ba
- Wani sabon littafi ya bayyana cewa rikicin kudin ya haddasa rashin jituwa a cikin jam’iyyar PDP
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon shugaban rikon kwarya na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya magantu kan binciken kudin makamai.
Magu ya bayyana dalilin da ya sa ba a gayyaci tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ba.

Source: Twitter
'Dalilin rashin binciken zargin makamai lokacin Jonathan'
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wani littafi mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammad Buhari” wanda Dr Charles Omole ya rubuta, cewar Daily Trust.
Rahoton ya ruwaito Ibrahim Magu na cewa an shirya binciken ne domin yi masa tambayoyi kan badakalar sayen makaman dala biliyan $2.1.
Magu ya ce ba a iya gayyatar Jonathan ba ne saboda takardu da bayanai sun nuna cewa kudaden da aka raba ba a amince da su a hukumance domin amfani da su wajen kamfen ba.
A cewar marubucin, Omole, wannan lamari ya sa wasu ke kallon tsohon Mashawarcin Tsaro na Kasa (NSA), Sambo Dasuki, a matsayin wani “shugaba na biyu” tare da Jonathan.
Marubucin ya ce an samu tashin hankali a cikin jam’iyyar PDP sakamakon zargin karkatar da kudaden, inda aka gayyaci shugabannin jam’iyyar da domin amsa tambayoyi.
Omole ya rubuta cewa:
“An samu rashin jituwa tsakanin NSA Sambo Dasuki da Ministan Tsaro, Aliyu Gusau, yayin da ikon sayen makamai da wasu muhimman ayyuka suka koma hannun NSA, abin da ya sa wasu ke kallon Dasuki a matsayin ‘mai juya akalar gwamnati’ tare da Jonathan.”

Source: Facebook
Yadda aka yi ta neman shugabannin PDP
Ya kara da cewa tsohon shugaban PDP na kasa, Adamu Mu’azu, yana buya, yayin da tsohon kakakin jam’iyyar, Olisa Metuh, ya gwammace yunwa ta kashe shi a kan mayar da N400m.
A cewarsa:
“Ana neman Adamu Mu’azu domin yi masa tambayoyi amma ya buya. Olisa Metuh kuwa, da aka tambaye shi kan N400m da aka biya wani kamfani da ke da alaka da shi, ya ce zai gwammace ya mutu da yunwa fiye da ya mayar da kudin; daga bisani aka kama shi.”
Omole ya kara da cewa an kama tsohon Darakta Janar na NIMASA, Patrick Akpobolokemi, ya tsere bayan beli, sannan aka sake cafke shi, har da tsare lauyan da ya tsaya masa a beli, cewar Daily Post.
An gargadi Jonathan kan takara a 2027
An ji cewa ana ganin cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan zai sake gwada sa'arsa wajen neman shugabancin Najeriya a zaben 2027.
Shugaban jam''iyyar ZLP na kasa, Dan Nwanyanwu , ya fito ya gargadi Jonathan kan biyewa masu son ganin ya kara da Bola Tinubu.
Nwanyanwu ya nuna cewa masu zuga tsohon shugaban kasar ba mutanen da za a yadda da su ba ne.
Asali: Legit.ng

