Da duminsa: An hana Magu gabatar da hujjoji gaban kwamitinin bincike

Da duminsa: An hana Magu gabatar da hujjoji gaban kwamitinin bincike

- Shugaban hukumar EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu ya gurfana gaban kwamitin bincike na fadar shugaban kasa

- Kwamitin na tuhumar Magu kan kadarori da kudaden da hukumar EFCC ta kwato daga hannun barayin kasa

- Wahab Shittu, lauyan Magu, ya ce an hanasu gabatar da hujjojin kariya gaban kwamitin

Wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa ya yi nuni da cewa tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da lauyansa Wahab Shittu a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli sun so gabatat da wata takarda mai dauke da shafuka 34 gaban kwamitin.

Takardun na dauke da hujjojin kariya ga Ibrahim Magu, sai dai rahotanni sun bayyana cewa an hanasu gabatar da hujjojin gaban kwamitin fadar shugaban kasar.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa Magu da lauyansa sun bayyana gaban kwamitin binciken dake karkashin mai shari'a Ayo Salami da misalin karfe 1 na rana har zuwa karfe 6 na yamma.

Rahotanni sun bayyana cewa ya isa fadar shugaban kasar tare da lauyansa Shittu da kuma wasu hadimansa.

Sai dai an ruwaito cewa Magu da Shittu ne kawai aka bari suka shiga cikin babban dakin gudanar da binciken, inda suka zauna na tsawon awanni.

Kundin hujjojin mai dauke da shafuka 34, ya kunshi hujjoji a rubuce, da hotuna, an kawo shi ne da nufin gamsar da kwamitin cewa duk tuhumar da ake yiwa Magu karya ce tsagoronta.

Jaridar Vanguard ta yi nuni da cewa lauyansa, Shittu, a wayar tarho ya ce ba a bari suka gabatar da wannan kundi ba a yau (Alhamis).

KARANTA WANNAN: Laifuka 10 da ake zargin Ibrahim Magu ya aikata a hukumar EFCC | Legit TV Hausa

Da duminsa: An hana Magu gabatar da hujjoji gaban kwamitinin bincike
Da duminsa: An hana Magu gabatar da hujjoji gaban kwamitinin bincike
Asali: UGC

"Amma dai zamu koma gobe (Juma'a)," a cewar lauyan, duk da cewa bai bayyana dalilin da ya sa aka hanasu gabatar da hujjojin ba.

Kwamitin fadar shugaban kasar na tuhumar Magu akan kadarori da kudaden da hukumar EFCC ta kwato daga hannun wadanda suka saci kudin jama'a.

A wani labarin; Iyalan Mrs Titi-Victoria Monde, tsohuwar kwamishiniyar watsa labarai ta jihar Nasarawa, sun sanar da mutuwarta a safiyar ranar Alhamis.

Mrs Titi-Victoria ta mutu tana da shekaru 62 a duniya. Mr Paul Abuga, kani ga Monde, ya bayyana labarin mutuwarta ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a Akwanga, karamar hukumar Akwanga da ke jihar.

Abuga, wanda shine sakataren karamar hukumar Nassarawa Eggon, ya ce Monde, wacce kuma ta kasance shugabar kwalejin ilimi ta Akwanga, ta mutu ne a babban asibitin Akwanga.

"Allah ya jikan ruhin yayata da kuma wadanda suka rigamu gidan gaskiya cikin salama da sunan Allah, Amen," a cewarsa.

NAN ta ruwaito cewa Monde ta rike mukamin kwamishiniyar watsa labarai ta jihar a shekarar 2011 karkashin mulkin tsohon gwamnan jihar Tanko Al-Makura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel