Abba Fiya: 'Dan Daban da Ya Kashe Mutum sama da 100 Ya Shiga Komar Yan Sandan Kano
- ’Yan sandan Kano sun cafke Abba Aliyu Fiya, matashi mai shekara 26 kuma fitinannen ɗan daba da ya addabi Kano, Legas da Fatakwal
- Abba Fiya ya amsa cewa ya shafe kusan shekaru bakwai yana harkar daba, yana ikirarin ba ya iya ƙirga mutanen da suka mutu sanadiyyarsa
- Ya ce sun yi amfani da makamai daban-daban, ciki har da wukake, adduna da bindigu, wasu daga Jamhuriyyar Nijar aka shigo da su
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da cafke Abba Aliyu Fiya, wani fitinannen ɗan daba mai shekaru 26 da ake zargi da addabar al’ummomi a sassan Kano, Legas da Fatakwal.
A wata hira da ya yi da rundunar yan sandan Kano, Abba Fiya ya lissafa wuraren da ya rika jan tawagarsa suna aikata ta'addanci da kashe mutane.

Source: Facebook
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ne ya tabbatar da kamen yayin wata hira da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
'Yan sandan Kano sun kama Abba Fiya
A zantawar, Abba Fiya ya bayyana cewa ya shafe kimanin shekaru bakwai yana harkar daba. Ya kuma amsa cewa ba ya iya tantance adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyarsa.
Abba ya jaddada wa yan sandan cewa mutanen su kan mutu ne wasu lokutan a yayin fadan daba, a wasu lokutan kuma washegarin fadan ne ake samun labarin sun mutu.
Ya ce:
"A fada ne, idan an sara, washegari sai ka ji an ce an mutu, an je an birne yan unguwa kaza. Da kuma wadanda za su debo sojojin haya, su ma su shiga fadan, na kashe wasu wadanda ba a san yan wace unguwa ba ne."
"A wurare koki ma haka, sun taho da yawa da makamai, mu ma mun taho, to idan aka fara fada, wanda ya juya ya fadi, kawai sai a sassara shi."
Matashin ya ce ya shiga harkar daba ne bayan an sare shi a lokacin da yake makaranta, abin da ya ce ya sauya masa tunani.

Source: Facebook
Abba Fiya ya kuma yi ikirarin cewa adadin mutanen da suka mutu sanadiyyarsa a Kano kaɗai na iya kaiwa kusan 100, duk da cewa hakan na daga cikin ikirarin da binciken ’yan sanda ke dubawa.
Wuraren da Abba Fiya ya kai hari
Dangane da aikata laifuffukan fashi, ya amsa cewa ya kwaci wayoyin salula da dama a sassa daban-daban na Kano.
Ya ambaci yankuna irin su Gangaren Dutse, Bachirawa da Ungogo, yana mai cewa bayan kwace wayoyin, sukan raba su tsakaninsu kafin a sayar.
Ya ce mahaifinsa bai san yana wannan harkar ba, yayin da mahaifiyarsa ta rasu tun da dadewa. Abba Fiya ya bayyana cewa sukan yi amfani da wukake, adduna, takubba da bindigu a fadan.
Ya kara da bayyana cewa wasu daga makaman da suke amfani da su ne aana shigo da su daga Yarji da wasu sassan Jamhuriyar Nijar.
A cewarsa, ya mallaki bindigogi guda biyu da ya samo a jihar Fatakwal, inda ya ce ana shigo da su ne a cikin kayan gwangwan.
Ya kuma lissafa wasu daga cikin abokan burminsa da suka rasu, ciki har da Wadata, S. Fulani da S. Dan Sani.
'Yan sanda sun ceto mutum 3 a Kano
A baya, mun wallafa cewa rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da samun nasarar ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su, a wasu samame guda biyu da ta kai a Kano da kuma jihar Kaduna.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce samamen na daga cikin matakan da rundunar ke ɗauka domin ƙarfafa yaƙi da miyagun laifuffuka.
Ya ƙara da cewa an gudanar da ayyukan ne bisa umarnin Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, wanda ya bayar da umarnin ƙara tsaurara matakan tsaro a fadin jihar da ma
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


