'Dan Majalisa, Bello El Rufai Ya Lale Miliyoyi domin Taimakon Karatun Mutane a Kaduna

'Dan Majalisa, Bello El Rufai Ya Lale Miliyoyi domin Taimakon Karatun Mutane a Kaduna

  • 'Dan majalisar Kaduna ta Arewa, Hon. Mohammed Bello El-Rufai ya saki ₦5m domin biyan kudin karatun daliban kwalejin fasaha ta Kaduna
  • Fitar da wannan tallafi a wannan lokaci ya sa ya kai jimillar ₦10m, kuma an sanya masa sunan gidauniyar ilimi ta Mallam Musa 'Director'
  • An kafa kwamitin da zai yi aiki tare da KADPOLY domin tabbatar da gaskiya da sauri wajen aiwatar da shirin bayanan fitar da aliban da za su amfana

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Hon. Mohammed Bello El-Rufai, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa a majalisar tarayya, ya sanar da shirin taimakon daliban mazabarsa.

Bello El-Rufa'i ya sanar da sakin N5m domin biyan kudin karatun daliban Kaduna ta Arewa da ke karatu a kwalejin fasaha ta Kaduna (KADPOLY).

Kara karanta wannan

Bayanai na kara fitowa a kan yadda gwamnati ta ceto daliban Neja

Bello El-Rufa'i ya tuna yan mazabarsa
Dan Majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufa'i Hoto: Bello El-Rufa'i
Source: Twitter

Hon. Bello El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar wallafa a shafin X a ranar Litinin, inda ya ce tallafin wani bangare ne na tsarin taimakon ilimi da ya dade yana aiwatarwa tun bayan da aka zabe shi.

El-Rufa'i ya tallafawa daliban KADPOLY

'Dan Majalisan ya bayyana cewa wannan shirin tallafi ba shi ne na farko ba, domin ya dade yana tallafawa dalibai a wani yunkuri na sauke nauyin da ke kansa.

Ya sanar da cewa Husseini Zubairu, Babban Mashawarci kan Harkokin Siyasa, shi ne Mai Kula da shirin. Nuhu Sani Lere, Babban Mashawarci kan Ilimi daga yankin Doka/Gabasawa, shi ne Shugaban Kwamitin.

Haka kuma ya ayyana Jibiril Abdullahi Belgium, Babban Mashawarci kan Ilimi daga shiyyar Kawo a matsayin Mataimakin Shugaba.

Bello El-Rufa'i ya kara kudi a asusun tallafawa daliban Kaduna
Hon. Bello El Rufa'i yayin zaman majalisa Hoto: Bello El-Rufa'i
Source: Twitter

Sauran 'yan kwamitin sun hada da Idris Deris, Shugaban APC na yankin Gabasawa; Ghali Waziri, tsohon Shugaban Ma’aikata ga Mukhtar Baloni; Maryam Sabo da Mary Wase.

Kara karanta wannan

Tsagin NNPP na son jawo matsala bayan babban taron su Kwankwaso a Abuja

Sauran su ne Hajiya Fati Sani One Minute; Sanusi Ali Muhammad; Ahmed Makama; Shamsu SS Adam; MD Gadzama; da Isiya Aliyu Kabala.

El-Rufa'i ya girmama Shugaban karamar hukuma

Ya kara da cewa an kafa asusun tallafin ne domin girmama marigayi Mallam Musa 'Director', wanda shi ne shugaban farko na Kawo Ward.

Ya ce sabon sakin kudin ya kara yawan asusun zuwa Naira miliyan 10, tare da jaddada cewa an riga an bayyana sunayen wadanda suka ci gajiyar zangon farko ga jama’a.

El-Rufa'i ya ce:

“Wannan ya kai jimillar asusun tallafin zuwa Naira miliyan 10. Kowa na da ‘yancin tantancewa ta hanyar duba shafukanmu na sada zumunta domin ganin yadda shirye-shiryen baya suka gudana. An kuma bayyana sunayen waɗanda suka ci gajiyar zangon farko ga jama’a. Tun daga lokacin, mun ci gaba da biyan kudin karatun wasu dalibai a makarantar daban-daban.”

Bello El-Rufai ya kuma bukaci dukkannin mazauna Kaduna ta Arewa da suka cancanta, ba tare da la’akari da jam’iyya, kabila ko addini ba, su nemi shiga shirin.

Hukuncin Nnamdi Kanu ya fusata Hon. El-Rufa'i

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, jigonta kuma tsohon kwamishina yar bar duniya

A wani labarin, kun ji cewa 'dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai, ya soki abin da ya kira rashin daidaito a yadda kotuna ke yanke hukunci kan mutanen da aka samu da laifin ta’addanci.

Hon. El-Rufai ya bayyana hakan ne a yayin zaman Majalisar Wakilai a Abuja, inda ya bukaci a yi kyakkyawan gyara a tsarin shari’a domin tabbatar da adalci da daidaito ga dukkanin masu laifin da aka kama.

Dan majalisar ya ce ya kamata tsarin shari’a ya kasance a bude, tare da tabbatar da cewa hukunci yana zama iri daya ba tare da nuna bambanci ba, musamman a shari’o’in da suka shafi tsaro da ta’addanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng