Sojoji Sun Cafke Hatsabibin Jagoran 'Yan Bindiga da Yake Addabar Jihohin Arewa

Sojoji Sun Cafke Hatsabibin Jagoran 'Yan Bindiga da Yake Addabar Jihohin Arewa

  • Dakarun rundunar sojoji ta 6 Brigade sun cafke fitaccen jagoran ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a yankin Benue–Taraba
  • An kama wanda ake zargin ne yayin wani samame na sirri a kauyen Vaase da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benue
  • Rundunar sojin ta ce kama shi babbar nasara ce a yaki da garkuwa da fashi da makami a yankin da ya dade yana kai hare-hare

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Dakarun rundunar sojojin Najeriya ta 6 Brigade, karkashin Sector 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS), sun cafke wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga.

An dade ana neman wanda aka kaman bisa zargin hannu a ayyukan garkuwa da mutane da fashi da makami a kan iyakar jihohin Benue da Taraba.

Sojojin Najeriya sun cafke wani dan ta'adda da ake nema ruwa a jallo.
Sojojin Najeriya da ke aikin kakkabe 'yan ta'adda a yankunan karkara. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Sojoji sun cafke jagoran 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin sama ta biya diyya ga iyalan bayin Allah da ta kashe a Sokoto

An gudanar da samamen ne a ranar 21 ga Disamba, 2025, karkashin sojojin FOB Wukari, bayan samun sahihan bayanan sirri, a garin Vaase da ke Ukum, jihar Benue, in ji rahoton The Guardian.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Litinin, hukumomin tsaro sun dade suna kokarin kama jagoran 'yan bindigar, Fidelis Gayama.

Mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Unar Muhammad, ya bayyana cewa binciken farko ya nuna Gayama na da alaka ta kusa da Aka Dogo, wanda ake nema ruwa a jallo a matsayin shugaban wata kungiyar ‘yan ta'adda.

Zargin ta’addanci a hanyar Kente–Wukari

Rundunar sojin ta ce ana zargin Gayama da jagorantar wata kungiyar masu laifi da ke addabar matafiya da al’ummomi a kan hanyar Kente–Wukari, tare da wasu yankunan kan iyakar Benue da Taraba.

Haka kuma, jami’an ‘yan sanda na Vaase Outpost sun tabbatar da cewa sunan Gayama na cikin jerin mutanen da sashen ‘yan sanda na Beji a karamar hukumar Ukum ke nema ruwa a jallo.

Rundunar ta tabbatar da cewa a halin yanzu Gayama na hannun sojoji, kuma za a mika shi ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi gaban kotu bisa doka.

Kara karanta wannan

Zamfara: Shaidanin dan bindiga, Isihu Buzu ya halaka bayan guntule masa kai

Kwamandan 6 Brigade na Sojin Najeriya kuma kwamandan Sector 3 OPWS, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa dakarun bisa kwarewa da jajircewar da suka nuna wajen cafke wanda ake zargin.

Sojoji sun ce za su ci gaba da kara kaimi wajen yaki da masu aikata laifuffuka.
Wasu jagororin rundunar sojojin Najeriya a lokacin da suke rangadi. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun durfafi 'yan bindiga

Birgediya Janar Uwa ya bayyana cafke Gayama a matsayin babban ci gaba a yaki da laifuffuka a yankin, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kai farmaki domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin dakile ayyukan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifi, in ji rahoton Premium Times.

Wannan na zuwa ne yayin da hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa an dauki tsauraran matakan tsaro gabanin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Dakarun Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a makonni biyu da suka gabata, inda suka kashe 'yan ta'adda da dama.

Baya ga 'yan ta'addan da aka kashe, dakarun sojojin sun kuma samu damar ceto mutum 67 da aka sace, tare da kama wasu 94 da ake zargi da aikata laifuffuka.

A cewar sanarwa rundunar, sojoji sun kwato bindigogi masu yawa, har da bindigogin zamani, manyan bindigogi, rokoki, bindigogi na gida da kayan hada bam.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com