Rundunar soji sun tura jiragen yaki 7 zuwa Benue da Taraba

Rundunar soji sun tura jiragen yaki 7 zuwa Benue da Taraba

Hukumar sojin sama na Najeriya tace ta tura jiragen yaki guda bakwai zuwa jihohin Benue da Taraba a aiki da take na Operation Whirl Stroke, domin magance rikicinmakiyaya da manoma a jihohin guda biyu.

Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya tabbatar da tura jiragen a Makurdi, jihar Benue, yayin wani kaddamar da jiragen a ranar Asabar.

Rundunar soji sun tura jiragen yaki 7 zuwa Benue da Taraba
Rundunar soji sun tura jiragen yaki 7 zuwa Benue da Taraba

A cewar Abubakar, jiragen da aka tura sun hada da jiragen yaki F-7 guda biyu, jirage masu tashi da saukar ungulu na Mi-35 biyu, wani jirgin ATR guda daya, jirgin 35 King daya da kuma jirgi mai tashi da saukar ungulu na Mi-35P daya.

KU KARANTA KUMA: An kama masu yunkurin kai hari kan Musulmi

Shugabansojin ya kuma ce, aikin da soji ke yi wanda ya hada da jihar Nasarawa zai kawo karshen rikicin makiyaya da garuruwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng