Gwamnati Ta Yi Nasarar Ceto Sauran Daliban Makarantar Neja 130 da aka Sace
- Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da kuɓutar ɗalibai da malamai 230 na makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri, Jihar Neja
- Sanarwar da Ma'aikatar yada labarai ta fitar ta bayyana cewa za a mika dalibai 130 da aka ceto ga gwamnatin jihar kafin a haɗa su da 'yanuwansu
- Mamallakin makarantar da aka kwashe masa dalibai, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya tabbatar da isowar ɗaliban a Minna ranar Litinin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa an ceto ɗalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri, Jihar Neja.
A cikin sanarwar da Ministan yada labarai, Mohammmed Idris ya tabbatar da haka, inda ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin nasara da ya kawo sauƙi ga ƙasar nan baki ɗaya.

Source: Facebook
A wata sanarwa da Ma’aikatar yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ta fitar, kuma aka wallafa a shafinta na X, gwamnati ta tabbatar da cewa an kuɓutar da dukkannin ɗalibai 230 da aka sace daga makarantar.
Gwamnati ta ceto daliban makarantar Neja
Daily Post ta wallafa cewa sanarwar ta ce kuɓutar ɗalibai 130 na ƙarshe ya kammala kawo karshen wani mummunan lamari da ya jefa iyaye, malamai da al’umma cikin tsananin fargaba tun bayan sace daliban a baya.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a mika waɗanda aka sako ga gwamnatin Jihar Neja, daga nan kuma a haɗa su da iyalansu domin su fara murmurewa daga raɗaɗin da suka fuskanta.
Ta yabawa jami’an tsaro bisa jajircewa da ƙwazon da suka nuna wajen aiwatar da wannan aiki mai haɗari, tana mai jaddada cewa hakan ya sake tabbatar da kudurin ƙasa na kare rayuka.
Gwamnati ta jajanta iyalan daliban Neja
A cikin sanarwar gwamnatin tarayya ta bayyana tausayi ga iyaye da masu kula da ɗaliban bisa wahala da tashin hankalin da sace yaran ya jawo musu.

Source: Twitter
Ta kuma yi masu fatan haɗuwa da yaransu a cikin annashuwa, tare da mika gaisuwar ƙarshen shekara da fatan Kirsimeti mai albarka ga iyalan da abin ya shafa.
A bangarensa, mamallakin makarantun St. Mary’s, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya tabbatar da cewa ana sa ran isowar ɗalibai 130 da aka ceto a Minna, babban birnin Jihar Neja, ranar Litinin.
Ya ce Gwamna Umaru Bago ya tuntube shi domin sanar da shi cewa an saki yaran da malamai, kuma za a tarɓe su a fadar gwamnatin jihar.
An ceto wasu daliban Neja a baya
A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta sanar da samun gagarumar nasara a ƙoƙarin da take yi na magance satar mutane, bayan ta ceto yara 100 daga cikin daliban da aka sace a Neja.
Wannan nasara ta zo ne bayan makonni biyu da sace daliban daga makarantar St. Mary da ke Papiri, a Karamar Hukumar Agwara ta Jihar Neja lamarin da ya jefa iyaye da sauran jama'a a fargaba.
An bayyana cewa babu wanda ke cikin mawuyacin hali, abin da ya rage radadin da jama’a suka shiga tun bayan faruwar lamarin, yayin da ake ci gaba da kokarin ceto sauran da ke hannun 'yan ta'adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

