Tinubu Ta Nuna Alhini bayan Mutuwar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

Tinubu Ta Nuna Alhini bayan Mutuwar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana alhini kan rasuwar tsohon Mataimakin Shugaban kasar Angola a Nahiyar Afirka wanda ya ba da gudunmawa sosai
  • An tabbatar da rasuwar Fernando da Piedade Dias dos Santos wanda Najeriya ta kira shi da ginshikin kwanciyar hankali da zaman lafiya
  • Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce marigayin ya taka rawar gani wajen gina Angola bayan ‘yanci, tare da inganta zaman lafiya da hadin kai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Nahiyar Afirka ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar tsohon mataimakin shugaban kasa a Angola.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana bakin cikinta matuƙa kan rasuwar tsohon Firayim Minista, Fernando da Piedade Dias dos Santos.

Tinubu ya jajantawa Angola kan mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasa
Marigayi Fernando da Piedade Dias dos Santos da Bola Tinubu. Hoto: Geraldo Sachipendo Nunda, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Gwamnatin Tinubu ta yi ta'aziyya ga Angola

Hakan na cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta wallafa a shafin Facebook wanda wakilin Legit Hausa ya gano.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Tsohon Sanata a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu labarin rasuwarsa da matuƙar baƙin ciki, tana yabawa gudummawarsa ga ci gaban Angola.

An bayyana marigayin a matsayin jagora mai tasiri wanda ya taimaka wajen kafa Angola ta zamani da bunƙasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kudancin Afirka.

Mukaman da marigayin ya rike a rayuwarsa

An haifi marigayi Dos Santos a ranar 5 ga Maris, 1950, sannan ya bar duniya a ranar 18 ga Disamba, 2025.

Ya yi aiki a muƙamai daban-daban na gwamnati tsawon shekaru, ciki har da Mataimakin Minista, Minista, Firayim Minista, Mataimakin Shugaba da Shugaban Majalisa.

Marigayin da aka fi sani da Nandó, ɗan siyasar ƙasar Angola ne, shi ne mataimakin shugaban ƙasar Angola na farko daga Fabrairu 2010 zuwa Satumba 2012.

Ya rike muƙamin Firayim Ministan Angola daga shekarar 2002 zuwa 2008, sannan ya zama shugaban Majalisar Dokokin Angola daga 2008 zuwa 2010.

Daga bisani, ya sake komawa wannan muƙami na shugaban Majalisar Dokoki daga 2012 zuwa 2022.

Fernando da Piedade Dias dos Santos, da ake kira "Nando,” ya kasance jarumin gwagwarmayar ‘yancin Angola da kuma jigo a siyasar ƙasar bayan ‘yanci.

Kara karanta wannan

Burkina Faso: Shugaba Traore ya saki sojojin Najeriya bayan ganawa da Tuggar

Tinubu ya fadi gudunmawar marigayi tsohon mataimakin shugaban kasar Angola
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

An fadi gudunmawar marigayi Dos Santos

Sanarwar ta ce shugabancinsa ya taimaka wajen jagorantar Angola a lokutan sauyi, sulhu da sake gina ƙasa bayan rikice-rikice masu tsanani.

Najeriya ta ce marigayin ya kasance abin girmamawa a Afirka, inda jajircewarsa ga haɗin kai, sulhu da ci gaba ta sa shugabanni da dama ke darajarsa.

A madadin Shugaba Bola Tinubu, Najeriya ta miƙa ta’aziyya ga Shugaban Angola, iyalan mamacin da al’ummar ƙasar, tana addu’ar Allah ya yi masa rahama.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka ya mutu

A baya, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban Amurka, Richard B. Cheney, ya rasu yana da shekaru 84 sakamakon ciwon huhu da zuciya.

Cheney ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu tasiri a gwamnatin Amurka, kuma ya taka rawa a mamayar Iraki a 2003.

Tsohon shugaba kasa, George W. Bush ya bayyana mutuwar Cheney a matsayin “rashi babba ga Amurka,” kasancewarsa “mai gaskiya".

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.