Labaran Duniya: Kasar Chad za ta biya Angola bashin $100m da dabobbi

Labaran Duniya: Kasar Chad za ta biya Angola bashin $100m da dabobbi

Kasashen Duniya sun samu labarin wani salon biyan bashi inda Chad ta shirya biyan Angola bashin da ta karba a hannunta, amma wannan karo ba da tsabar kudi ba.

Kamar yadda mu ka samu labari daga wata jaridar kasar Angola, gwamnatin Chad za ta biya Angola makudan bashin da ake bin ta na fala miliyan 100 da tarin Tumaki.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan yarjejeniya da aka cin ma ya yi wa duka kasashen daidai. Chad ta na fama da karancin kudi, yayin da ake neman Tumaki a Angola.

Chad ta ci wannan bashi ne a shekarar 2017 amma yanzu ta na fama da matsalar kudi. Kasar Kudancin Afrikan kuma ana ta bangare, ta na neman dabbobi bayan wani fari.

Rahotanni sun bayyana cewa fiye da shanu 1, 000 su kai so babban birnin kasar Angola na Luanda a cikin tsakiyar Watan Maris. Bisashen ne za su biyawa Chad bashin kudinta.

Labaran Duniya: Kasar Chad za ta biya Angola bashin $100m da dabobbi

Akwai dabbobi a kasar Chad, abin da aka rasa a Angola
Source: Twitter

KU KARANTA: Cutar COVID-19 ta kashe wani Likitan Najeriya da ke aiki a Turai

Jaridar nan ta Jornal de Angola ta fitar da rahoto kwanaki cewa Chad ta fara ba kasar Angola wadannan shanu 1,000 ne domin rage nauyin tulin bashin da ya taru a kanta.

Ana sa ran cewa Angola za ta karbi Tumaki 75, 000 a cikin shekaru goma a hannun kasar ta Chad. Yarjejeniyar ta nuna Angola ta karbi kowace dabba ne a kan fam Dala 1, 333.

Idan aka yi lissafi a kudin Najeriya za a ga cewa bisashen sun tashi ne a kan kusan N500, 000. Jimillar kudin da Angola ta ke bin Angola a Naira ya haura Naira Biliyan 370.

Kasar Chad da ta yi iyaka da Najeriya za ta sake aikawa Angola dabbobi 3, 500 kwanan nan. Sannu a hankali kasar za ta yi ta turawa Angola dabbobi har an fanshe bashin.

Duk da cewa Angola kasa ce mai arzikin danyen mai a Duniya, rikicin yakin basasan da ta shiga na tsawon shekaru 27 ya jefa ta cikin matsala kamar yadda BBC ta bayyana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel