An Ki Saye a Kasuwa, Tinubu Ya Ci gaba da Hawa Jirgin Saman da Obasanjo Ya Sayo
- Shugaba Bola Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa jihohin Najeriya uku kafin hutu na musamman saboda bikin Kirsimeti da ya saba yi
- Tinubu ya ziyarci jihar Borno domin kaddamar da ayyuka kafin zuwa Bauchi da kuma Lagos domin gudanar da hutun Kirsimeti
- Tinubu ya yi tafiyar a cikin jirgin Boeing 737 da aka mallaka tun zamanin Olusegun Obasanjo, wanda aka taba tallata shi kasuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bar Abuja a ranar Asabar 20 ga watan Disambar 2025 domin ziyarar aiki da hutun Kirsimeti.
Tinubu ya isa jihar Borno inda zai wuce Bauchi domin jaje game da rasuwar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Source: Twitter
Mai ba Bola Tinubu shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a jiya Juma'a 19 ga watan Disambar 2025.
Ziyarar Tinubu zuwa Borno, Bauchi da Lagos
Tinubu ya tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 11:45 na safe, inda zai fara ziyarar aiki a jihohi da kuma hutun ƙarshen shekara.
Shugaban zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda zai je Bauchi domin ta'aziyyar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Kafin zuwansa, rundunar ’yan sandan jihar Borno ta ce ta tura jami'an tsaro na musamman, masu sa ido da kuma jami’an sashen lalata abubuwan fashewa (EOD) domin tabbatar da cikakken tsaro a jihar.

Source: Twitter
Tsohon jirgin sama da Tinubu ya hau
An ce Tinubu ya je Borno ne inda ya hau tsohon jirgin Boeing 737 mai shekaru kusan 20 wanda aka gaza saya tsawon lokaci da yake shanye a kasuwa.
Amfani da tsohon jirgin saman na zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo ya tabbatar da komawar jirgin aiki ba tare da sanarwa ba, cewar Punch.

Kara karanta wannan
An sanya dokoki a gari saboda ziyarar da Bola Tinubu zai kai gidan Sheikh Dahiru Bauchi
An fitar da jirgin ne a kasuwa a watan Yulin 2025 amma aka janye shi daga sayarwa saboda rashin masu saye da kuma yadda aka yi tayin farashi.
Gwamnatin Tarayya ta sayi jirgin ne a shekarar 2005 kan kuɗin dala miliyan 43, kuma ya yi aiki a gwamnatoci da dama har zuwa watan Agustan 2024, lokacin da gwamnatin Tinubu ta karɓi sabon jirgin Airbus A330-200 da aka sabunta.
A cewar manyan jami’an fadar shugaban ƙasa, an janye jirgin daga kasuwa ne bayan masu saye sun fara tayin farashi har ƙasa da dala miliyan 10, abin da bai dace da hasashen gwamnati ba, duk da gyare-gyaren da aka yi masa a Switzerland.
An saka jirgin shugaban kasa a kasuwa
A baya, an ji cewa jirgin fadar shugaban kasa kirar Boeing 737-700 da aka saka a kasuwa tun watan Yuli, 2025, bai samu mai saye ba har yanzu.
Kamfanin JetHQ na kasar Amurka, wanda ke da alhakin tallata jirgin, ya tabbatar cewa har yanzu jirgin yana nan a kasuwa.
An shirya sayar da jirgin ne bayan gwamnatin Bola Tinubu ta fara tsarin rage kashe kudi da kuma rage yawan jiragen shugaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
