Tinubu Zai Je Jihohi 3 kafin Hutun Kirsimeti, Ya Fadi Abin da Zai Kai Shi

Tinubu Zai Je Jihohi 3 kafin Hutun Kirsimeti, Ya Fadi Abin da Zai Kai Shi

  • Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja gobe Asabar 20 ga watan Disambar 20245 domin ziyarar aiki a wasu jihohi
  • Tinubu zai je jihohi biyu kafin ya karasa Lagos domin gudanar da hutun Kirsimeti da kuma na karshen shekara
  • Shugaban ƙasa zai shafe hutun ƙarshen shekara a Lagos, inda ake sa ran zai halarci bikin gargajiya na Eyo a filin tar na Tafawa Balewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai tashi daga Abuja ranar Asabar 20 ga watan Disambar 2025 domin ziyarar aiki zuwa wasu jihohi.

Jihohin da shugaban zai ziyarta kafin hukun Kirsimeti sun hada da jihar Borno, Bauchi da kuma Lagos inda zai yi hutu.

Tinubu zai je jihohi 2 a Arewacin Najeriya
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tinubu zai bar Abuja domin ziyartar wasu jihohi

Legit Hausa ta samu wannan rahoton ne daga mai ba shi shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga wanda ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Tsofaffin 'yan majalisa sun kawo wanda suke fatan ya zama gwamnan Kano a 2027

Sanarwar ta ce a jihar Borno, ana sa ran Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da wasu manyan ayyuka da Gwamna Babagana Umara Zulum ya aiwatar tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya.

Haka kuma, Shugaban ƙasa zai halarci bikin ɗaurin auren Sadiq Sheriff, ɗan tsohon Gwamnan Jihar Borno kuma Sanata, Ali Modu Sheriff, da amaryarsa Hadiza Kam Salem.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai tashi daga Abuja ranar Asabar domin ziyartar jihohin Borno, Bauchi da Lagos.
A jihar Borno, Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Babagana Umara Zulum tare da Gwamnatin Tarayya suka aiwatar.
Haka kuma, zai halarci bikin ɗaurin auren Sadiq Sheriff, ɗan tsohon Gwamnan jihar kuma Sanata, Ali Modu Sheriff, da amaryarsa, Hadiza Kam Salem."
Tinubu zai ziyarci jihohi 3 a Najeriya
Bola Tinubi a cikin jirgi yana shirin barin Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Abin da Tinubu zai je yi jihar Bauchi

Daga Maiduguri, Tinubu zai wuce jihar Bauchi domin miƙa ta’aziyya ga gwamnatin jihar da kuma iyalan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, shugaban darikar Tijjaniyya, wanda ya rasu ranar 27 ga Nuwambar 2025.

Bayan ziyarar ta’aziyyar, Shugaban ƙasa Tinubu zai wuce jihar Lagos, inda zai shafe hutun ƙarshen shekarar 2025 da muke ciki zuwa sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

Cakwakiya: Tinubu ya shiga rudani da aka tafka kuskure a taron APC a Aso Rock

Yayin zamansa a Lagos, ana sa ran Shugaba Tinubu zai kasance babban bako na musamman a bikin gargajiya na Eyo da aka shirya gudanarwa ranar 27 ga Disamba a dandalin Tafawa Balewa.

Rahotanni sun ce bikin Eyo zai karrama fitattun mutane da suka haɗa da marigayiyar mahaifiyar Shugaban ƙasa, Alhaja Abibatu Mogaji, tsohon Gwamnan Lagos, Alhaji Lateef Jakande, da kuma Cif Michael Otedola.

Tinubu ya jaddada yaki da ta'addanci

Mun ba ku labarin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta fara aikin kafa sabon tsarin tsaron kasa domin murkushe ta'addanci.

Shugaban kasar ya jero wasu kungiyoyi da suka dauki makamai, ya ce daga yanzu dukansu za a dauke su a matsayin 'yan ta'adda domin daukar mataki.

Tinubu ya bai wa 'yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.