Bayanai Marasa Dadi Sun Bayyana kan yadda Ake Juya Tunanin Buhari a Mulkinsa
- Marubuci Charles Omole ya bayyana yadda wasu na da ke kira 'Cabals' ke juya tunanin marigayi Muhammadu Buhari
- Ya ce mutanen har sun yi karfin da sukan dasa labarai a jaridu domin shugaban kasa ya karanta sabanin abin da ke faruwa
- Omole ya bayyana cewa dukkan shugabannin Najeriya tun shekarar 1999 suna da irin wadannan da ke tasiri a gwamnati
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Lauya kuma marubuci, Charles Omole, ya bayyana irin tasiri da 'Cabals' ke da shi a mulkin Muhammadu Buhari.
Ya ce mutanen da ke kusa da marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan dasa labarai a jaridu domin ya karanta.

Source: Facebook
Omole ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 18 ga watan Disambar 2025 yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels TV.
Yadda 'Cabals' ke da tasiri a gwamnatoci
Da yake karin haske kan abubuwan da ke cikin littafin, Omole ya ce dukkan shugabannin Najeriya tun 1999 suna da masu karfin fada a ji.
Ya ce wadannan mutane na taka rawa wajen tsara manufofi da tasiri kan yadda gwamnati ke tafiya.
Omole ya bayyana cewa kasancewar irin wadannan kusa da shugaba ba lallai ba ne abu mara kyau.
A cewarsa, idan kungiyoyin suna da muradin da ya dace da na shugaba, za su iya taimaka masa wajen cimma manufofinsa.
Sai dai ya ce matsala tana tasowa ne idan kungiyoyin suna da manufarsu ta kansu.

Source: Facebook
Yadda 'Cabals' suka cika gwamnatin Tinubu
Lauyan ya ce a gwamnatin Buhari, akwai gungun mutane masu karfi da ke da cikakken tasiri, suna juya akalar gwamnati.
Amma a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Omole ya ce akwai gungun irin wadannan 'Cabals' daban-daban har biyar.
Ya lissafa da ce cewa sun hada da ta Femi Gbajabiamila, mutanen Seyi Tinubu, bangaren Remi Tinubu, bangaren sakataren shugaban kasa, da kuma wata kungiya da Tinubu kansa ke jagoranta.

Kara karanta wannan
Dalung ya liasafo matsaloli 4 da cire tallafin man Tinubu da ya yi ya jawo a Najeriya
“Kamar yadda na fada a cikin littafi na, duk shugaban kasa tun 1999 yana da mutane da ake kira 'Cabals'.”
- In ji Omole.
Ya ce tsarin gwamnatin Tinubu ya fi rikitarwa saboda yawan masu karfin fada a ji da ke kusa da shi.
Omole ya ce Buhari mutum ne da ke matukar son karanta jaridu tun daga lokacin yana soja, cewar TheCable.
'Cabals' sun sha sauya tunanin Buhari kan Najeriya
A cewarsa, akwai rahotannin da ke cewa wasu daga cikin kungiyoyin sun kai ga kirkirar jarida domin dasa labaran da Buhari zai karanta.
Ya ce bambanci tsakanin gwamnatin Buhari da ta Tinubu shi ne yawan gungun mutanen da ke tasiri.
Omole ya kammala da cewa wannan yanayi na da alfanunsa da kuma illolinsa, gwargwadon yadda ake sarrafa shi.
'Ana amfani da sa hannun Buhari' - Fatima
A wani labarin, Fatima Buhari ta ce an gano takardun gwamnati da ke dauke da sa hannun bogi na marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.
Fatima ta ce wasu jawabai da umarnin Buhari ana sauya su bayan ya amince da su, lamarin da ke nuna tasirin wasu a cikin gwamnati.
Littafin tarihin marigayi Buhari ya bayyana cewa tsohon shugaban ya yi zargin ana leken asiri a ofishinsa a Aso Rock Villa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
