An Sanya Ranar da Bankin Duniya Zai Ba Najeriya Sabon Rancen Dala Miliyan 500
- Bankin Duniya na shirin amincewa da rancen dala miliyan 500 ga Najeriya domin kara saukin samun kudi ga kananan 'yan kasuwa
- Rancen zai gudana ta hannun bankin BDN na Najeriya, yayin da ‘yan kasuwa masu zaman kansu za su samar da mafi yawan kudin
- Shirin FINCLUDE zai taimaka wajen kirkirar sababbin hanyoyin bada bashi, rage hadari ga masu ba da rance, da habaka tsarin kudi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ana sa ran Bankin Duniya zai amince da rancen dala miliyan 500 ga Najeriya a yau Juma’a, a wani yunkuri na fadada damar samun kudi ga kanana da matsakaitan kamfanoni a fadin kasar.
Rahotanni daga Bankin Duniya sun nuna cewa shirin da aka ware domin 'yan kasuwa a Najeriya (FINCLUDE), zai jawo ra'ayin masu zuba jari tare da kirkirar sababbin hanyoyin tallafa wa ‘yan kasuwar.

Source: Facebook
Yadda za a samar da rancen kudaden
Ana sa ran kwamitin gudanarwar Bankin Duniya zai amince da rancen a ranar 19 ga Disamba, 2025 kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin kudin, $400m zai fito daga bankin kasa da kasa kan gine-gine da samar da ci gaba (IBRD), yayin da $100m zai zo daga kungiyar samar da ci gaba ta kasa da kasa (IDA).
Gwamnatin Tarayya ce za ta karbi rancen, yayin da bankin samar da ci gaba na Najeriya (DBN) zai kasance hukumar da ke kula da aiwatar da shirin FINCLUDE gaba daya.
Jimillar Kudaden da Najeriya za ta karba
Jimillar kudin da ake bukata domin aiwatar da shirin FINCLUDE ya kai dala biliyan 2.39, in ji wani rahoto na Nigeria Communication Week.
Daga wannan adadi, ana sa ran bankuna da masu zuba jari ne za su samar da sauran dala biliyan 1.89 ba tare da wani tallafi kai tsaye daga gwamnati ba.
Bankin Duniya ya bayyana cewa wannan tsari zai taimaka wajen rage dogaro da gwamnati kadai, tare da kara kwarin gwiwar masu zuba jari wajen bada rance ga kananan kamfanoni.

Source: Getty Images
Yadda aka tsara shirin FINCLUDE
A cewar Bankin Duniya, shirin zai yi amfani da tsarin aiki na bankin samar da ci gaba na Najeriya da reshen sa mai suna ICGL domin saukaka rance da rage hadarin da ke tattare da ba da bashi ga kananu da matsakaitan 'yan kasuwa.
Shirin FINCLUDE ya kasu kashi uku:
- Na farko shi ne kirkirar hanyoyin bada bashi masu sassauci da suka dace da bukatun kananan kamfanoni daban-daban.
- Na biyu shi ne rage hadarin bada rance, wanda zai sa bankuna su kara yarda su bada rance.
- Bangare na uku shi ne tallafin fasaha, wanda zai mayar da hankali kan zamantar da tsarin kudaden kananu da matsakaitan kamfanoni a Najeriya, ciki har da amfani da fasahar zamani wajen tantance masu rance da bibiyar kudade.
Bola Tinubu ya karbo bashin $9.65bn
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Bola Tinubu ta karbo bashi daga Bankin Duniya a shekarar 2023 zuwa 2025, da ya kai dala biliyan 9.65.
Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya za ta karbi sabon rancen dala miliyan 500 daga Bankin Duniya kafin ranar Juma'a, 19 ga watan Disamba, 2025.
Daga 2023 zuwa 2025 bashin da aka karbo daga Bankin Duniya karkashin IDA ya kai $7.30bn yayin da bashin IBRD ya kai $2.35bn da kuma tallafin $122.19m.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


