NLC: Ajaero Ya Fadi Sabon Alkawarin da Tinubu Ya Dauka game da Rashin Tsaro

NLC: Ajaero Ya Fadi Sabon Alkawarin da Tinubu Ya Dauka game da Rashin Tsaro

  • Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya dauki alkawarin daukar karin matakai kan matsalar tsaro
  • An yi taruka tsakanin Shugabannin kwadago da Shugabannin gwamnati domin dakile zanga-zanga da suka fara a garuruwa
  • Duk da tattaunawa, 'yan kungiyoyin kwadago sun fito zanga-zanga a Legas da Abuja domin tunawa gwamanti akwai matsala

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masu alkawura a kan magance rashin tsaro.

Ajaero ya tabbatar wa shugabannin kwadago cewa gwamnatinsa na daukar matakai na musamman domin shawo kan karuwar matsalar rashin tsaro a fadin kasar nan.

NLC ta ce Tinubu ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro
Jagororin kwadago a Najeriya, a gefe kuma Shugaban Kasa Bola Tinubu Hoto: NLC Headquarters/Bayo Onanuga
Source: Twitter

The Cable ta wallafa cewa Ajaero ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Kasa a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yadda zanga zangar 'yan kwadago ke gudana a Kano, Sokoto, sauran jihohi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta gana da wakilan Bola Tinubu

Shugaban NLC ya sake yin karin bayani ne a cikin daren Laraba, bayan wata ganawa ta biyo baya da tawagar gwamnatin tarayya wadda gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya jagoranta.

Sauran m'yan awagar sun hada da gwamnan Kebbi, Nasiru Idris, gwamnan Edo, Monday Okpebholo, gwamnan Kogi, Usman Ododo, da kuma karamar ministar kwadago da samar da ayyukan yi, Nkiru Onyejeocha.

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa ganawar ta kasance wani yunkuri na karshe da nufin hana zanga-zangar kasa baki daya da NLC ta shirya yi sakamakon tabarbarewar tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.

Kungiyar NLC ta koka da matsalar tsaro

A cewar Ajaero, Shugaba Tinubu ya jaddada cewa matsalar rashin tsaro ba za ta dade tana addabar Najeriya ba, yana mai cewa gwamnati na daukar karin matakai domin dawo da zaman lafiya.

Shugaban NLC ya ce Shugaban kasa ya kuma amince cewa tsaro ba ya tsaya kan 'yan bindiga kawai ba, har da tsaron tattalin arziki na ma’aikata.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya albishir kan matsalar rashin tsaro

Ajaero ya ce matsalar tsaro ta ishi 'yan Najeriya
Shugaban Kwadago Joe Ajaero da wasu 'yan NLC yayin wata zanga-zanga a Najeriya Hoto: NLC Headquarters
Source: Facebook

Joe Ajaero ya ce shugabannin kwadago za su koma su yi wa mambobin NLC bayani kan abin da aka cimma a ganawar da aka yi da shugaban kasa da tawagar gwamnati.

Ya kara da cewa an amince a sake zama a watan Janairun 2026 domin tattauna wasu muhimman batutuwa da har yanzu ba a warware su ba.

Sai dai duk da wadannan tattaunawa, rahotanni sun nuna cewa 'yan kungiyoyin kwadago sun fito zanga-zanga a wasu manyan birane ciki har da Legas da Abuja.

Yadda 'yan NLC suka yi zanga-zanga

A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta aiwatar da zanga-zangar kasa baki daya da ta shirya domin nuna damuwa kan karuwar matsalolin tsaro da ke addabar ‘yan Najeriya.

Zanga-zangar ta fara ne a safiyar Laraba, 17 ga watan Disamba, 2025 inda 'yan kungiyar suka taru a wurare daban-daban a fadin kasar, musamman a manyan birane daga ciki har da Kano da Legas.

Kara karanta wannan

"Karya kake yi," Tsohon gwamnan Sakkwato ya maida martani mai zafi ga Bello Turji

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin kashe-kashe, sace-sace da garkuwa da mutane a jihohi da dama, lamarin da NLC ta ce ya kamata a kawo karshensu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng