Asiri Ya Tonu: 'Dan Majalisar Tarayya Ya ‘Gano’ Makirci a Dokar Sabon Haraji
- 'Dan majalisa mai wakiltar mazabun Kebbe/Tambuwal, Abdussamad Dasuki, ya yi zargin sauya wasu bayanai na sabon dokar haraji
- Hon. Dasuki ya yi zargin cewa an sauya wasu sassa na dokokin haraji bayan Majalisar Tarayya ta amince da su a kwanakin baya
- 'Dan majalisar ya ce kwafin da aka fitar a hukumance ya bambanta da wanda da Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa suka amince
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wani dan Majalisar Wakilai, Abdussamad Dasuki, ya ja hankalin ‘yan majalisa kan zargin cewa an yi sauye-sauye a dokokin haraji.
Hon. Dasuki ya ce an yi sauyin ne bayan Majalisar Tarayya ta amince da su wanda Bola Tinubu ya turo gabanta.

Source: Twitter
Zargin dan majalisa kan dokokin haraji
'Dan majalisar ya bayyana haka ne a zaman majalisa a yau Laraba 17 ga watan Disambar shekarar 2025 da muke ciki, cewar rahoton Punch.
Dasuki ya ce kwafin dokokin haraji da aka wallafa a hukumance ya bambanta da wanda da Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa suka daidaita kuma suka amince da ita.
Ya ce:
“Na tashi tsaye a yau saboda an take min hakki a matsayina na dan wannan muhimmiyar majalisa. Mun amince da wadannan dokokin haraji a wannan zaure. Na dauki lokaci na tsawon kwanaki uku ina duba kwafin da aka wallafa.”
Dasuki ya kara da cewa ya duba kundin kuri’u da shawarwarin Majalisar Wakilai, tare da komawa Majalisar Dattawa domin duba sigar da aka daidaita tsakanin bangarorin biyu.
Masanin tattalin arzikin ya ce abin da aka amince da shi a zauren majalisa ba shi ne abin da aka wallafa ba, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.
“Na ba da kuri’ata, an kirga ta, amma yanzu ina ganin wani abu dabam."
- In ji shi.
Ya bukaci Kakakin Majalisar Wakilai da ya duba bambancin da ke tsakanin abin da aka amince da shi da abin da ke cikin kwafin da aka wallafa, yana mai cewa ‘yan Najeriya na ganin wani abu daban a hukumance.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Source: Facebook
Abin Hon. Dasuki ke bukata daga majalisar
Dan majalisar na Kebbe/Tambuwal ya nemi a sake duba dokokin, yana mai cewa dukkan takardu su koma gaban Kwamitin da ke da alhakin haka domin a yi gyare-gyaren da suka dace.
Ya bayyana lamarin a matsayin keta kundin tsarin mulki da dokokin kasa.
“Wannan keta kundin tsarin mulki ne, kuma bai kamata wannan majalisa ta yi shiru ba."
- Cewar Dasuki
A nasa bangaren, Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce majalisar za ta binciki batun tare da daukar matakin da ya dace domin kare muradin kasa.
Haraji: Tinubu ya kwantar da hankulan mutane
An ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kara yin magana game da sababbin dokokin haraji da ake shirin farawa a sabuwar shekarar 2025.
Tinubu ya kwantarwa ’yan Najeriya hankulansu game da sababbin dokokin haraji da aka kawo domin ci gaban kasa da al'umma.
Shugaban ya yi karin haske cewa dokokin haraji za su amfani talakawa, masu ƙaramin albashi da ’yan kasuwa a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
