Monguno Ya Tona yadda Aka Dakile Shi a Mulkin Buhari, Ya Kira Sunayen Mutum 2
- Tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan lamuran tsaro ya bayyana matsalar da aka samu a mulkin Muhammadu Buhari
- Babagana Monguno ya ce wasu miyagu a fadar shugaban kasa sun raunana aikinsa a zamanin mulkin marigayi Buhari
- Ya bayyana cewa rikici kan sauya kamfanin da ke samar da mai ga jiragen shugaban kasa ya bankado wasu sirruka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), Babagana Monguno, ya tuna matsalolin da ya fuskanta a baya.
Monguno ya bayyana cewa 'cabals' a fadar shugaban kasa sun yi ta raunana ofishinsa a lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari.

Source: Facebook
Matsalolin da Monguno ya fuskanta a mulkin Buhari
Monguno ya fadi haka ne a cikin littafin tarihin Buhari mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, wanda Charles Omole ya rubuta, cewar TheCable.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, wata shawara ta tsaro da ya bayar kan sauya kamfanin da ke samar da mai ga jiragen shugaban kasa, ta tona asirin wasu muradun sirri da suka yi katutu a fadar Aso Rock.
Monguno ya ce ya rubuta wasika zuwa ga Buhari, ya hada da rahoton kwamandan, tare da ba da shawarar a sauya kamfanin, kuma shugaban kasa ya amince da hakan.
Sai dai ya ce wannan mataki ya fusata Abba Kyari, tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, wanda ya tambaye shi cikin fushi.
Ya ce:
“Me ya sa ka yi haka?”
Ya ce ya amsa masa cewa idan wani lamari ya faru kuma ya yi shiru, to laifin zai rataya a wuyansa.
Arangamar Monguno da Mamman Daura
Monguno ya kara da cewa an shigo da kamfanin tun zamanin Olusegun Obasanjo ne a matsayin na wucin gadi, amma daga baya ya samu gindin zama a gwamnatoci da dama.

Kara karanta wannan
'Buhari ya yi zargi ana bibiyarsa': 'Yarsa ta fadi yadda suke magana a boye a Aso Rock
Ya ce Mamman Daura, dan uwan Buhari, ya ziyarce shi daga baya inda ya bayyana matakin a matsayin zalunci ga kamfanin, tare da tambayar dalilansa.
A cewarsa, rikicin ya kara tsananta har ya zama kamar abokin gaba a wajen Mamman Daura.
Ya ce har Ministan Kudi, wanda ke biyayya ga Daura, aka shigar cikin lamarin, inda aka rika hana ofishin NSA kudade duk da amincewar Buhari.
“Buhari da ‘yan Najeriya duka sun zama wadanda cabal suka zalunta, sun tara dukiya fiye da kima.”
- In ji Monguno.

Source: Facebook
Yadda aka hana ofishin Monguno kudi
Monguno ya ce hana ofishinsa kudade ya raunana tsarin tsaron kasa, tare da makantar da gwamnati wajen gano barazana, cewar Punch.
Ya bayyana cewa kudin da ya gada daga magabacinsa sun kare, yayin da biyan kudin tsarin leƙen asiri da haɗin gwiwa da ƙasashen waje suka tsaya cik.
Ya ce ana kula da na’urorin sa-ido a fadar shugaban kasa ne da kudin NSA, amma duk wani yunƙurin sabuntawa ana toshe shi.
Ya ce ya rubuta fiye da wasiku 30, tare da kai ziyara kai tsaye wurin Buhari, amma shugaban kasa kan ce masa:
“Ka bar fayil din,” ko kuma “Na tura wa Malam Abba.”
'Dalilin Buhari na sauya fasalin Naira'
An ji cewa sabon littafi da aka wallafa ya bayyana dalilin da ya sa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake fasalin Naira.
Wani bangare na littafin ya ce an yi sauyin fasalin ne domin dakile sayen kuri’u, ba don cutar jam’iyya mai mulkin Najeriya ba.
Littafin ya ce hukumomin tsaro sun nuna damuwa kan rawar da kudi ke takawa a zabe, inda EFCC ta gabatar da shawarar takaita amfani da tsabar kudi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
